INEC ta zayyana Matakai 7 da ya zama dole kowanne mai zaɓe ya bi

  • 1- za’a fara gudanar da ayyukan zaɓe da misalin karfe 8:30am a kowacce rumfar zaɓe.
  • 2- malaman zaɓe zasu fara da karɓar katin zaɓen kowanne mai yin zaɓe don tantance katin da na’urar BVAS.
  • 3- Malaman zaɓe zasu tantance sunan kowanne mai zaɓe don tabbatar da yana daga cikin wadanda zasu kaɗa ƙura’ar su a wannan rumfar zaɓen.
  • 4- zasu ƙara tantance tambarin yatsa na kowanne mai zaɓe da na’urar BVAS don tabbatar da mallakar Katin da mai kaɗa ƙura’a ya gabatar.
  • 5- Malaman zaɓe zasu baiwa kowanne mai zaɓe takardar kaɗa ƙuri’a kala biyu data zaɓen shugaban kasa da kuma ta zaɓen ɗan Majalisar wakilai.
  • 6- Mai kaɗa kuri’a zai garzaya gurin da aka tanada don dangwalawa ɗan takarar da yake so, kuma dole ne gurin ya kasance mai sirri dakuma tsaro.
  • 7- Bayan kammala kaɗa kuri’a mutun zai bar farfajiyar zaɓen nan take har saiya kai tazarar mita 300 tsakanin sa da rumfar zaɓe, hakan zai bada damar tabbatuwar tsaro a filin zaɓe.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!