Kada Ku Afka Ramin ‘Yan Damfara Domin Sun Ɓullo Da Sabon Salo
A ko wanne lokaci ana samun ƙorafe-ƙorafe a bankunan mu da muke ajiya musamman abinda ya shafi damfara duba da yadda yan damfara suka fito da wani sabon salo na kiran wayar customer ko kuma tura masa sakon kartakwana wato SMS ta wayar salula.
Shidai wannan sabon salo na damfara sukan turo da saƙon na wayar salula wanda yake ɗauke da kalamai na cewa kasamu nasarar samun tsabar kuɗi har Naira 70,000 ko 80,000 amma bazaka iya karɓar wannan kudin ba har ba sai ka kira Mr. Eze ko makancin haka a waya sannan sai ka karɓa
Dan haka duk wanda yaga irin wannan saƙo kada yayi saurin miƙa musu dukkan abinda suke nema a wajen sa domin kuwa zasu iya yahse asusun mutum nan take.
Wani sa’in kuma sukan kira ne direct su bukaci kaba su wasu code da suke turowa shima sukan yiwa mutum daɗin baki cewa wai daga bankin ka ne kuma abin ba haka yake ba, dan haka idan an sami irin wannan shima sai a hanzarta izuwa bankinka mafi kusa domin yin bayani ga customer care, inda zasu kara maka bayani.
Salon cutar kullun ƙara bazuwa yake cikin al’umma dan haka muna kira ga mahukunta da waɗanda suke da al’haki akan irin waɗan nan abubuwa da suke faruwa a wannan lokaci da su taimaka wajen dakile wannan zamba da ake yiwa ‘yan kasa.
Allah ya karemu daga sharrin masu yaudara da dukkan wani nau’in cuta.