KADAN DAGA CIKIN ALAMOMIN CIWON SANYI NA MATA

  • Fitan ruwa, wanda zai iya zuwa kamar ruwa amma yellow ko green tsinkakke. Ko kuma ya fito a fari ko in ce milk mai kauri sosai
  • Wanda wannan ruwan zai haddasa miki ƙaiƙayi a al’aurarki har ma da jikinki wani. Ki yi ta susa har wurin yayi ja. Haka nan in ya fara shahara sai ruwan ya fara wari mai tada hankali
  • Daga nan sai ya feso miki da kuraje masu azabar ƙaiƙayi. Wanda in ya tsarga in baki wasa ba ko a cikin jama’a ne sai kin sosa.
  • Ciwon mara da baya, wani ma yana sanya ciwon kai, jin amai, ko yin laulayi kamar mai ciki
  • Dashewar gaba ki ji kamar kin ƙone, haka nan zaki ji kamar ana tsungulinki a cikin al’aurarki da wajensa
  • Bushewar gaba koda ke budurwa ce zaki jiki a bushe a bushe. Matar aure kuma saukar ni’ima sai ya rinka mata wahala koda ta sha abun ni’imar
  • Ɗaukewar sha’awa gaba ɗaya ko kiji kina yi kaɗan kaɗan. Kuma duk wani abun da zaki ci da ya kamata ya saukar miki da ni’ima zaki ga ke baki ganin komai
  • Jin kamar tana ko tsutsa yana miki ya mararki ko ki ji motsinsa a gabanki
  • Fashewar kafa, ki ga kullum ƙafarki akwai faso ko kauje wani infection ne ke sakawa
  • Rikicewar al’ada koma rashin zuwansa gaba ɗaya ko sanya miki ciwon ciki. Ga mutuƙar buɗe mace ga budurwa ko matar aure, zaki yi ta neman maganin tightening amma ko kin yi zaki buɗe saboda infection. Dama wasu da babu adadi ko wacce da kalar nata.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!