KO KINSAN TARIN AMFANIN KANUMFARI GA JIKINKI

Ko kinsan tarin amfanin da Kanumfari ya keyi a jikin Mace? Yau ya kamata ki sani

Kamar yanda mata ke ajiye Zuma a gida haka yanzu mata basa rabuwa da kanunfari domin duk wani hadin daka na musamman ko hadin ruwan jaraba ko wani tsumi idan kuka bincika zakuga akwai sa hannun kanunfari don haka kema ki ajiye shi don burge mijinki.

Duk lokacinda zaki dafa shayi kada kimanta dashi domin idan ya hadu da lefton yana aiki a jikin mace wajen karin ni’ima kuma ya na da kyau yajinki ya zama akwai kunfari aciki

Ana Amfani da kanimfari wajen rage tumbi ki jika shi aruwa idan ya yini ajike sai kishanye ruwan ki kara wani zaki ga cikin ki ya saki kinyi bayan gida wannan shine alamar yayi miki aiki.

Ana Amfani da Kanimfari wajen maganin infection idan kika saka ruwa tafasashe a flast sai ki zuba shi aciki da ganyen magarya kirufe sai yayi kamar sa’a daya (1 hour) zaki yini kina yin tsarki dashi har zuwa dare.

Zaki iya daka garin kanimfari ki hadashi da totuwar raken dakika sha yabushe sai ki sami farin muski (miskul dahra) ki cakuda shi sosai da garin da totuwar raken da kuma muskin idan ya bushe sai ki ringa turaren tsugunawa dashi wannan kada ki barshi.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!