SIRRIKAN HABBATUS-SAUDA

Wanda yake fama da matsalar pimples ko kurajen fuska, ya samu lemon tsami ya gurje kurajen dashi. Bayan minti 5 sai ya sanya ruwan dumi ya dunduma fuskarsa dashi. Sannan ya shafeta da Man habbatus sauda.

Insha Allahu Qurajen zasu rabu dashi. Kuma ba zasu bar masa Bakaken tabo afuskarsa ba.

H/SAUDA tana maganin sanyin Qashi da ciwon gabobi idan aka dumama man-ta, sannan amulke dukkan gabobin dashi.

Wanda yake fama da matsalar TSUTSAR CIKI, ya samu gurasa ya rika cinta da man H/sauda. Insha Allahu tsutsotsin zasu mutu gaba daya. Kuma zai samu lafiya da izinin Allah.

Matsalar CIWON KAI MATSANANCI, asamu Man h/sauda ashafa agoshin marar lafiya. Zai wartsake nan take insha Allah.

Matsalar CHUSHEWAR CIKI, KO KUMBURIN CIKI, KO ULCER, asamu cokali 3 na man h/sauda agauraya da zuma chokali 6.
Marar lafiyan yasha cokali 3 safe da rana da yamma. Insha Allahu za’a samu Lafiya

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!