Kula da Kibar Jiki

Kula da kibar jikinki abu ne mai tasirin gaske wajen kara miki lafiya da kyau. Sannan tara kitse a jiki na daga cikin manyan abubuwan da suke haifar da manyan cututtuka kamar cutar suga [diabetes], hawan jini [hypertension] da dai sauransu.

Hanyoyin rage kiba da samun lafiyayyen jiki:

  • Cin nama kadan. Ka maida nama ya zama kadan cikin abincinka maimakon ya zama da yawa.
  • Ka nemi madara mara mai ko kitse da yawa. Ka rage abinci da ya kunshi nono ko madara mai yawa; maimakon haka, yi amfani da mara kitse da yawa.
  • Lura da ciye-ciyen ki. Ka zabi kayan ciye-ciye marasa mai da yawa. A maimakon haka ka rika cin karas , busassun abinci, da ganyaye a madadin masu mai da yawa kamarsu soyayyen dankali.
  • Rage mai da ya jike sharaf a girki. Yi amfani da ruwan mai a madadin busashshe.
  • Ki rage amfani da manja da mankoko. Yawancin wannan mai yana jike ne, amma yawancin wannan suna dauke da kitse sosai. Yi amfani da man suya, da sauransu.
  • Rage abinci mai kitse. Yi kokari kaci abinci dake da mai kasan 200 mg a kowacce rana. Rage cin kwai zuwa guda hudu a sati.
  • Ki kara yawan abinci mai bada karfin jiki. Kara abinci mai kawo karfi – kamarsu ‘ya’yan itace da kayan gona, da abinci masu kwaya da ya hada da wake busasshe, da suke da abubuwan Karin karfi
  • Kici ‘ya’yan itace da ganyaye. Domin kiyaye zuciyar ka, kaci ‘ya’yan itace da ganyaye.
  • Kayi amfani da kwayoyin hatsi. Kwayoyin hatsi na rage cututtukan zuciya. Suna cikin kayan lafiya na jiki, kuma hanyar samun abinci mai gina jiki, amma yi hankali domin suna kawo kiba.
  • Kara yawan kifi cikin abincinki. Kasashe masu yawan cin kifi suna da raguwar mutuwa daga kowacce damuwa, haka ma daga cutar zuciya.
  • Akwai wata ‘’yar na’ura ko damarar ‘tummy trimmer’ da mata ke amfani da ita domin rage kibar tumbi; idan an sanya wannan abu za a rage yawan ci, sannan a rage kibar tumbi.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button