Maganin sanyin Mara (infection) fisabilillah

Abubuwan bukata
- Ruwan zam zam
- Tumeric
- Kanunfari
- Citta
- Tafarnuwa
Yadda za’a hada
Da farko uwargida Zaki samo duk wadanan kayayyakin saiki yankasu kanana daidai ,kafin nan amman Sai an kankare bayan ,kuma Sai a cire bawon tafarnuwan
Saiki zo ki samu roba ko wacce iri ce amman mai marfi saiki dakko wadanan kayayyakin da Kika yanka saiki zuba a wanan robar ,saiki dakko ruwan zam zam a zuba dai dai musali amman kada asa yayi yawa yafi karfin kayayyakin .
Saiki ajiye tsawon kwana 1 da wuni daya ,sai a dinga shan karamin kofi 1 da safe ,ayi haka har tsawon sati 3 insha allahu za’a Samu waraka .
Gargadi :a ajiye maganin a wuri mai sanyi ,kuma banda yara kada a basu susha, ko mai ciki ,kuma Sai anci abinci kafin a sha ,masu ciwon ulcer kuma Sai sun saka zuma kafin su sha .
Wanan shine :ku cigaba da kasancewa tare damu a kowane lokaci
Mungode