MATSALAR CIWON YOYON FITSARI ( VVF ) DA YADDA ZA’A MAGANCE SHI
Wannan wata matsalace da ta zama ruwan dare musamman ga mata masu zaman karkara dalilin rashin zuwa asibiti lokocin na’uda.
A karkara zakaga mace takai kwana uku tana nakuda amma an barta a gida ana mata jiko Wanda hakan ba taimakonta zaiyi ba.
Abubuwa guda uku da suke kawo matsalar yoyon fitsari sune:
- Doguwar nakuda,
- Yiwa mata kaciya da kuma
- Yiwa mata yanka ko kari yayin haihuwa
Wannan matslalar anfi samunta ta sanadiyar doguwar na’uda ta dalilin ko kugun matar matsatse ko kuma kan jaririn nekato ne.
Idan kugun matar matsattse ne ko dan karami kuma kan jariri daidai yake, to kugun zai rike kan jariri ya kasa fitowa. Hakama idan kugun uwa daidai yake wato wadatacce ne amma kan jariri kato ne.
to kan jariri zai makale ya kasa wucewa. Idan dayan biyun ya faru, maimakon mace tai nakuda cikin โyan awoyi, sai ta yini ta kwana, wato nakuda ta zama doguwa kenan. To wannan yakan sa kan jariri ya rika gogar fatar da ta raba mafitsara da wurin
haihuwar ta koke, fitsari ya fara yoyo, kuma a mafi yawan lokuta akan rasa jaririn saboda wannan matsi.
MATSLAR DA AKE FUSKANTA IDAN MACE TA SAMU WANNAN MATSALAR
- Mutanen anguwa zasu kyamace ta.
- Mijin ta zai guje ta.
- Da matsaloli kala kala
Saboda haka Mata, Maza , Iyaye, Likitocin karkara aiki ya samemu, yazama wajibi akan mu mu tausaya mata, mudinga karantar da matan karkara zuwa:
- Awon juna biyu.
- Haihuwa a asibiti.
Allah Ta’ala Yatsare Dukkanin Mata Daga Wannan Ciwo.
Lafiya uwar jiki
Please share after reading
Don’t edit don Allah