Mene ne web 3.0?
“Web 3.0: Fasahar “Blockchain” (3)
Ana amfani da manhajar “Smart Contract” wajen rajistar inshora, da taskance bayanan marasa lafiya a asibitoci, da yin rajistar lasisin motoci, da taskance bayanan kadarorin jama’a, da taskance bayanan da suka shafi kayayyakin abinci da wasu kamfanoni ke yin odarsu tun daga gona har zuwa inda za a sarrafa su. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 27 ga watan Mayu, 2022.”
-Baban sadik
Ba iya nan ya tsaya ba web 3 ya haɗa da:
- Semantic web: wato fadada ilahirin yanar gizo ta duniya world wide web, cikin wannan tsari ne har machine ko muce komfuta zata iya mu’amala da wata komfutar.
- Dapps: Decentralized application wasu manhajoji ne da za’a kirkira a wannan juyi na canjawar yanar gizo izuwa web 3, inda manhajojin zasu kasance babu masu cikakken iko akan su face mamallakan su.
- Masu aiki da manhajajoji su kasance masu sarrafa bayanan su yanda suke so.
- NFTs: wannan bayanan sa yana gaba. Amma a takaice kadarori ne da abubuwan amfani na yau da kullum da ake mai da su NFTs None Fungible Tokens kenan, wato zasu kasance masu halayya irin na zahiri amma kuma acikin waya ta hanyar hoto, kuma kowanne yana da shedar mallaka ta yanda wani bazai iya kwaikwaya ko ya kwace na wani cikin sauki ba, misalan abubuwan da ake maida su NFTs sun hada da: zane, gida, mota, injin mining GPUs da sauran su. Mutum yakan iya turawa mutum ko a ina yake kasancewar yana tafiya ne akan tsarin fasahar blockchain.
- AR/VR: wannan shine abinda zakuga an kirkira mutum yana iya sawa a fuskar sa, kamar tabarau amma yafi tabarau girma, yana ganin hoto ko video na wani waje ko dai Game, yayinda zai ji kamar a wajen yake.
- Shiga blockchain ba tare da izinin kowa ba.
- Artificial intelligence (AI): wannan fasaha ce da mutum zai iya tattaunawa da komfuta kuma ta bashi amsar abinda ya tambaya cikin sauƙi.
Da sauransu…
Web 1.0 ko web 1 a duniyar yanar gizo ta world wide web a taƙaice ya kasance zamani ne daga 1991 zuwa 2004, yayinda a wannan lokacin ake amfani da tsayayyun shafuka waɗanda ake kira da “static pages”, a takaice dai zamu iya kiran wannan lokacin da mafarin sanuwar yanar gizo a duniya.
Shi kuwa web 2.0 ko web 2 ya fara ne daga 2004 har izuwa yanzunnan, zamani ne da yake ɗauke da idea ta abinda ake ƙira web a matsayin platforms wato “web as platforms” kenan, shine lokacin da mutane suke ƙirkiran rubutu ko wata maƙala su ɗaura a dandalin tattaunawa wato “forums”, yanar gizo “social media”, network services, blogs, da kuma wikis da dai sauran su.
Kamar yanda muka sani daga shekara ta 2008 muka fara jin wani tsari da ake kira “blockchain technology” wanda akayi amfani da tsarin “cryptography ” aka gina kudin da ake kira da “cryptocurrency” waɗannan kuɗaɗe suna gudanuwa ne kan tsarin “blockchain” inda zaka iya turawa mutum kuɗin ko a ina yake a fadin duniya ba tare da neman izinin kowa ba. Zamuyi bayani a fadade a gaba.
Kamar yanda muka sani shi wannan tsarin kuɗi yakan wakilci kuɗaɗe ne da muka sani wato “fiat” irin su dollar, pound, euro, da ma waɗanda bamu sani ba kamar su bitcoin, Ethereum, bnb, ltc, da dai sauran su.
To shi wannan tsari na web 3 yazo ne da gamayyar “cryptocurrency” da kuma abinda ake kira da “non-fungible tokens” wato NFTs, mun riga da munyi bayanin “cryptocurrency” a baya.
Zamu cigaba…