MESA KORAFIN RASHIN WARKEWA YAYI YAWA DAGA CIWON SANYI (VAGINAL INFECTION)


Idan Namiji da Matar sa suna dauke da wannan cutar,
abinda ya dace dukkansu biyu za sufara shan magani, bawai matar kadai ba, muddin daya cikinsu ne yake shan magani akoi matsala, dan da wuya a warke daga ciwon sanyi (vaginal infection)

Idan kuna saduwa (jima’i) lokacin da kuke shan magani to wuya a warke daga ciwon sanyi (vaginal infection). Wanda kuma Idan sun fara shan magani to ba a saduwa har sai an kammala shan magani.

Idan kinada abokiyar zama (kishiya) amma ba a daurasu akan maganin ba, to dawuya a warke daga ciwon sanyi (vaginal infection). Idan mijinki yanada mata fiye da daya to dole abokiyar zamanki (kishiyarki) ita ma a daurata akan maganin koda bata da ciwon, kuma suma sauran matan a daurasu akan maganin koda ku hudu ne. Sannan babu saduwa (jima’i) lokacin da ake shan magani.

Rashin kammala adadin kwanakin da aka gindaya nashan maganin. Misali ace asha na kwana bakwai, sai mutum yasha na kwana uku idan yasamu sauki sai yadena shan maganin. Muddin kwayar cutan basu mutu ba to zasu dawo. Don haka ana kamalla adadin kwanakin shan magani da aka gindaya wa mutum.

Duk matar da aka daurata akan magani duk zanda ta cire wandonta yakamata ta wanke ta da antiseptic kafin ta maido, wannan shima yana taimakawa wajen warkewa.

Idan akaci gaba shan magani kuma ba’a kiyaye wassu hanyoyin da suke kawo wannan cutar ba shima akwai matsala
sosai, domin da wuya a warke daga ciwon sanyi (vaginal infection).

Please share after reading

Don’t edit don Allah

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!