sabbin sirrikan WhatsApp na karshen shekarar 2022
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wanan lokacin cikin wannan sabon darasin, a yau inshallah zamuyi bayani ne akan wasu muhimman sirrika guda uku wanda suka sake futo a karshen shekarar na ta 2022 na tabbata wadannan sirrikan zasu burge ku a lokacin da kuke amfani da whatsApp dinka.
Da farko kafin ka shiga whatsapp dinka neman wadannan sabin sirrikan ka fara shiga playstore na wayarka kayi updated din whatsapp sai kayi updated din whatsapp shine idan ka shiga whatsapp zai bayyana ma wadannan sabin sirrikan.
SIRRI NA FARKO
APP LANGUAGES
WhatsApp zasu baka dama kayi amfani da yaren da kakeji sakamakon da kafin suyi Updated dinsa saidai kayi amfani da yaren English kadai koda kana gane yaran turanci ko baka gane wa so amma yanzu zasu baka dama kayi amfani da duk yaran da kakeso.
zaka danna wannan Digo digon guda uku na fuskar whatsapp dinka kana danna wannan saika danna settings kana danna settings daka kasa zakaga inda akasa App Languages to nan ne bangaran da zaka iya chanja dikannin yaran da kakeso.
SIRRI NA BIYU
STARRED MESSAGE
WhatsApp a yanzu zasu baka dama ka zabi wani message mai mahimmanci ka killace shi misali idan a group aka turo sakon kai kuma wannan sakon ya burgeka domin kada ka rasa wannan sakon zaka danna kan wannan sakon ka danna masa Star sakamako group ana turo sakonni da yawa bayan wani lokaci idan ka shiga group neman wannan sakon kafin ka gano shi zaka sha wahala idan kuma ka dannawa sakon Star kana shiga bangaran Star zaka ganshi.
zaka danna wannan Digo digon guda uku na fuskar whatsapp dinka daga barin hannunka na dama kana dannawa zakaga inda akasa ( Starred Message ) to a nan ne zakaga dikkanin wani sako daka danna masa Star.
SIRRI NA UKU
SEARCHING
WhatsApp zasu baka dama idan kana chat da mutum kuma kuna group daya dashi ka gano dukkanin messages din daya tura a group din koda kwa messages din yakai shekara 10 a lokaci daya kodakwa group din yakai 10.
Kawai zaka danna wajan Searching a whatsapp din naka ka rubuta sunan sa kai tsaye zasu bayyana dukkanin messages din daya tura a group da kuma chat din da kukayi dashi koda kwa yakai shekara 10.
ku dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha
mungode