Shawara zuwa ga Waƴanda zasu cika neman aikin Federal Road Safety (FRSC)

Hukumar Road Safety Zata Dauki Sabbin Ma’aikata Na Shekarar 2023

Yana da kyau kafin mutum yacika ko wanne kalar portal ya tabbatar yakaranta dokoki da ka’idoji kafin yafara saka bayanan sa domin gujewa kuskure, soboda kuskure ƙalilan ke sa ayi disqualified na mutum. Ku tuna mutane kusan milyan ne zasu cika sannan mutum dubu biyar kacal za a ɗauka aciki, kun ga dole sai wanda ya cika ka’idoji ne zai samu shiga.

Akwai wasu abubuwan da idan kasamu kuskure wajen cikawa automatically computerr (programming) su zatayi disqualified naka tunda, misali wajen (Health challenge “yes/no”, idan kasaka “yes” kaga babu batun jiran tsammani yakare. Da kuma wajen height sunce no less than 1.67m idan kasaka kasa da haka shima dai automatically disqualified ne, da sauransu).

Sannan akwai wasu abubuwan lura sosai, sannan suna da mutuƙar muhimmanci, kamar haka:

Passport (photo): yana da matuƙar kyau kasaka decent photo, photo mai kyau, babu hula, babu eyes glass, sannan a buɗe ido raɗau a photon.

Email: yana da kyau Email naka yazama matured, kada kayi amfani da email wanda kasa ka nickname a jiki, misali princessai9@mail.com koh wani ashguy7@gmail.com da sauransu, email naka yakasance sunanka ne.

Address: wannan yana da muhimmanci sosai, wajen saka address kusaka hadda numbar gida da layi, bawai kawai sunan gari zaku saka ku wuce ba.

Shekaru: shekarun ka kada yaban banta da najikin NATIONAL identity Number NIN, sannan kada su wuce 35.

Da sauransu, sai mu kiyaye su.

Babban abu mai muhimmanci shine addu’a bayan mun cika. Allah yasa mudace.

Repost:
Manu Abba Gana Gumsa

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!