Takaitaccen Bayani Da Hukumar NDLEA Tayi Ga Wadanda Sukayi Apply Na NDLEA 2023

TAKAITACCEN BAYANI DA HUKUMAR HANA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN KWAYOYI TA KASA TAYI(NDLEA)
wasu batutuwan da aka tattauna a sararin Twitter

1.Tambayoyin jarrabawa za su kasance iri ɗaya ga ƙwararru da sauran ayyuka sai dai lauyoyin za su sami wasu tambayoyin dan a bambanta da Kuma gwada ƙwarewar aikin su.

2.Za’a dauki  manyan jami’ai, 1,200 da kuma kananun  ma’aikata 3,800 ga karamar jami’a.

3.Ana iya rubuta jarabawar a kan wayar hannu da computer daga kowane yanki like

4.Yan takara za su iya rubuta jarabawar a kowane lokaci tsakanin karfe 10 na safe zuwa 11:59 na rana na ranar da aka tsara Wanda aka tura musu.

5.Za a yi tambayoyi a kan Turanci, Maths da General papers.

6.hanyar da zaka bi wajan Sanya I’d  dinka Koda ka manta  shi ne zakai amfani da NIN number dinka akarshe kamar haka NDLEA/SUPT/2023/NIN
A ciki portal din

7.Babu takamaiman adadin tambayoyin da za a yi har sai kun shiga jarrabawar.

8.Za a fara amfani da portal ne kawai daga ranar Litinin.

9.Jarabawar tantancewa shine kashi na farko na aikin daukar ma’aikata. Sauran matakan za su haɗa da tambayoyin gwajin jiki da gwajin ƙwayoyi.

10.Ba za a nunawa kowa  makin sa ba. Amma 80% shine alamar wucewa.

11.Idan an gayyace ka sau biyu, irin wannan mutum ya yi amfani da kwanan wata da lokacin farko. Duk wani ƙoƙari na rubuta jarabawa sau biyu zai hana mai nema cancanta.

12.Ana ci gaba da aiko sakon  gayyata.Wasu sakon da aka tura musu sun koma baya Don haka Suna tsare tsaren  wasu matakai don isa ga waɗanda har yanzu ba su samu ba, irin su matakan SMS/Email

13.Tambayoyin da ake ya dawa a baya na karya ne kuma bai kamata a dogara da su ba.

14.Masu HND za su fara daga 7 sannan BSC za su fara da  8.

15.Za a gudanar da gwajin lafiyar jiki kamar yadda aka tanadi cibiyoyi 5. Don haka za a tantance masu neman nasara a cibiyar da ke kusa da su.

16.wannan shine link din jarabawa Koda ba kaga sako ba ta email ka gwada jarrabawa ta hanyar Sanya I’d din ka
https://cbtservices.online/Login-Candidate
©️Engr Zaharadden
#tv5_kura

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!