AMFANIN HABBATUSSAUDA WANDA YA KAMATA KU SANI

Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana

Ana kiran Habbatus-sauda da sunaye da yawa, misali ana kiranta da”Habbatul Baraka” da larabci, wato kwaya mai albarka. Da turanci kuma ana kiran ta da ‘the blessed seed’, Black Cumin, Nigella Sativa, Black Caraway da sauransu.

Binciken ya dangata habbatus-sauda da matukar amfani wajen magance cututtuka daban-daban, sannan ta na taka muhimmiyar rawa wajen kiwon lafiya, cikin yardar Mai Duka.

Ana samun Habbatus-sauda daga ‘ya’yan tsiron “Nigella sativa”. Hakanan an gano cewa, Shekaru aru-aru da suka gabata dubun-dubatar al’ummar nahiyar Asia da Afirka ke amfani da ita a fannin kiwon lafiya da kuma magance wasu cututtuka dake addabar jikin dan-adam.

Ba tare da bata lokaci ba, ga jerin magunguna 31 da ake samu daga wannnan tsiro mai albarka, da fatan a sha karatu lafiya, sannan da fatan za’a jarraba domin gane wa ido amfaninta.

Matsalar Tsakuwar Koda/Mafitsara; Ana amfani da Habbatus Sauda domin fitar da tsakuwar koda ko ta mafitsara. Yadda za a hada wannan maganin shine, a samu habbadus sauda mai kyau, da kuma zuma marar hadi, sai a cakuda su sannan a zuba ruwan zafi a rinka sha. Da yardar Allah za a samu waraka. Hakanan za a iya amfani da wannan hadin don kawar da matsalar fitsari musamman ga maza tsofaffi dake fama da wannan matsala.

Maganin Ciwon Kai; An tabbatar da cewa, ta na magance ciwon kai. Domin samun wannan fa’ida sai a hada garin habbatus-sauda da ruwan Kal, ake sha sannan kuma a dinga digawa a hanci don samun afuwa daga matsanancin ciwon kai.

Samar Da Isasshen Ruwan Nono Ga Mace Mai Shayarewa; Wani lokacin akan samu mace ta haihu amma kuma ta rasa isasshen ruwan nonon da za ta shayar da jaririnta, idan har haka ta kasance, sai a samu garin habbatus-sauda a hada ta da madara, mace mai shayarwar ta rinka sha, idan Alllah Ya yarda za ta samu isasshen ruwan nonon da za ta shayar da jaririnta.

Maganin Tsutsar Ciki; Habbatus-sauda na maganin tsutsar ciki. Ga duk mai fama da wannan matsala sai ya samu garin habbattus sauda ya gauraya ta cikin ruwan kal ya ke sha.

Kara karfin Garkuwar Jiki; Wani bincike da wasu masana su ka gudanar kan habbatus-sauda ya tabbatar da cewa, yawan amfani da ita na da matukar muhimmanci wajen karawa garkuwar jikin dan adam karfi.

Rigakafin Kamuwa Daga Cututtuka; Wani bincike ya gano cewa, yawan amfani da Habbattus-sauda wata hanya ce ta magance duk wata cuta da ka iya yiwa jikin dan Adam barazana. Ta na yin wannan aiki ne ta hanyar samar wa da jikinmu garkuwa mai karfi ta yadda cutukan da kan kai wa jiki hari ba za su iya tasiri gare shi ba.

Dakile Yaduwar Kwayoyin Cuta Cikin Jiki; Hakanan wani bincike da aka gudanar kanta ya bayyana cewa, ta na dakile girman kwayoyin ccuta a jikin mutum, baya ga haka ta na hana yaduwar kwayoyin cutar ga sassan jikinmu

Wallahu a’alamu

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!