SIRRIN DAKE TATTARE DA AYA(TIGERNUT)

Ga wasu daga cikin amfanin sinadaran da aya ta kunsa
- Tana dauke da sinadaran magnesium da calcium da kuma iron
- Tana samarwa da jiki sinadarin protein da kuma lafiyayen kitse
- tana kunshe da sinadarin vitamin B wanda ya ke amfanar da fata da gashi da kuma farata
- Don samarwa da jiki sinadaran vitamin da minerals, ya na da kyau a rika cin gram 70 zuwa 50 na Aya a kullum
- Aya tana da amfani saboda tana kara karfin garkuwar jiki sinadarin carbohydrates
- ta yawan amfani da ita, za ka gano cewa kusan ba ka rashin lafiya kuma za ka ji dadi sosai
- aya na inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita kuruciya, tana karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzari na zahiri da na boye
- -Haka kuma aya tana da amfani ga sha’anin da ya shafi ciki da hanji, tana dauke da sinadarin da ke hana cushewar ciki da kuma kumburi
- Aya na taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral (maikon cikin jini) mara kyau a cikin jini.