AMFANIN GANYEN SHUWAKA GA LAFIYAR DAN ADAM.
Mutane da dama kan yi amfani da shuwaka ne kawai a matsayin ganyen miya, amma in an yi amfani da ganyen yadda ya kamata, akwai magunguna da dama a jikinsa. Masana harkokin bincike kan magunguna na kalifa herbal medicine and marriage councelling munyi matukar bincike kuma mun gano cewar ganyen shuwaka na dauke da sinadarai da dama da ke magungunan cututtuka daban-daban kamar haka.
Ciwon Hanta. Ganyen shuwaka magani ne mai kyau na ciwon hanta ana amfani da shi kamar haka: A samo abarba da ba ta nuna ba, sannan a samo ganyen yazawa (cashewy guda goma, sai cikin tafin hannu na ‘ya’yan auduga, sai kwalba goma na ruwa wanda za a tafasa. A rinka sha cikin babban cokali daya kullum har kwana goma.
A Markada namijin goro guda 20 har ya zama gari sannan a zuba cikin ruwan lemon tsami (Lime juice) a kawo kwalba daya na zuma mai kyau a hada su duka a waje daya a gauraya. A rinka shan babban cokali daya (dessertspoon) sau hudu a rana har na tsawon watanni biyu.
Markade ganyen shuwaka guda 40 a zuba cikin ruwa mai kyau da ya kai lita 4 a rinka shan kofi guda sau 3 a rana har na tsawon watanni biyu. Wannan yana magani sosai na ciwon hanta, in ruwan ya dade ana iya sake wani sabon jikon.
Zazzabi A tafasa busasshen ganyen shuwaka (gram 10) a samo gram 25 na busasshen garin TUMARIC a dafa a cikin ruwa kofi daya har sai ya tafasa. Tun da duminsa sai a sanya zuma cokali daya, daga nan bayan ya huce sai a sha sau uku a rana. Yana warkar da zazzabi sosai.
Sankara (Cancer) Kari (Kulun Da Ke Fita A Jiki) Shan ruwan da aka tatse daga ganyen shuwaka yana taimakawa wajen rage girman kari da jinkirtar da girman kwayoyin cutar sankara. Shan ruwan yana domin yana kara karfin garkuwan jiki.
Hawan Jini Ruwan ganyen shuwaka na taimakawa wajen rage yawan gishiri a jikin mutum domin yana dauke da sinadarin ‘potosium’ mai yawa, hakan kuma na kawo saukin hawan jini.
Ciwon Siga Yawan shan ruwan ganyen shuwaka a kaidance yana saukar da yawan su da ke cikin jini don haka na rage karfin cutar sugar. Ga yadda ake sha domin maganin hawan jini da na siga: A samo rabin cikin tafin hannu na ganyen shuwaka sabon tsinka, a wanke sannan a dafa a ruwan da ya kai kofi 3. Za a rinka shan ruwan sau biyu a rana.
Kaikayin JIKI. A samu gram daya na ganyen shuwaka da gram daya na garin citta a markade har sai ya zama gari sai a sanya a cikin ruwa mai kyau a gauraya a rinka sha sau uku a rana. Yana maganin kaikayin jiki sosai.
Maleriya. A samo ganyen shuwa cikin tafin hannu a dafa a ruwa kofi hudu har sai ya kone ruwan ya zamo kamar saura kofi biyu sai a rinka sha sau uku a rana.
Ciwon Afendis (Appendicitis) A samo busasshen ganyen shuwaka gram 30 da ruwa 400ml da zuma mai kyau cikin babban cokali sai a dafa har sai ya kone ruwan ya zamo rabi sai kuma a sauke a kara cokali guda na zuma kuma in ya yi sanyi sai a rinka sha sau uku a rana a kai a kai.
Zazzabin Shawara (Typhoid) Haka kuma shuwaka na maganin typhoid in an sha kamar haka. A samo ganyen shuwaka guda 10 zuwa 15 a dafa har sai ruwan ya rage kofi daya sai a bar shi ya yi sanyi sannan a zuba masa zuma a rinka sha a kai a kai kofi daya a kullun.
Ciwon Kunne Shuwaka na maganin ciwon kunne sosai. A samo ganyen shuwaka (fresh) a markade shi sai a rinka diga ruwan digo uku a kunnen da ke ciwo sau uku a rana kuma za a yi hakan har na kawanaki 4 zuwa 5. Wannan ganye na shuwaka yana yin magungunan cututtuka da dama. Sai dai kuma a lura cewa idan aka sha har yawansa ya wuce kai’da yana da illoli a jiki; kamar sanya ciwon kai, gudawa da sauransu. Da fatan za a yi amfani da shi yadda ya dace dan Allah duk wanda ya karanta wannan sako to ya watsama duniya domin amfanuwar yanuwa musulmai wannan faida tasamo.