TIKTOK ZAI FARA KARBAN KUDI GA TIKTOKERS MASU YIN LIVE VIDEO

TikTok sun kirkiri yin subscription ga masu yin Live

Ranar Monday din nan ne TikTok yace zai fara karbar kudi ga masu yin live, ta hanyar yin subscription

Kamar yadda sauran ababen sadarwa na media suke samun kudi to irinsu Facebook and Instagram, Shima TikTok bazai yi kasa a guiwa ba zai fito a dama dashi tsakanin wadannan platforms da suke gasa da juna wajen burge mabiyansu.

TikTok yace wannan tsari na subscription an gabatar da shine cikin wannan satin, Kuma hakan zai shafi creators wato masu popular account duk lokacin da zasuyi live to dole sai da sub. Sannan a yanzu ne yake ga wasu da aka zaba but nan gaba Zuwa wata uku to zai zamo game gari ne ga kowa da kowa a duk inda yake. Sai dai har yanzu company bai fadi adadin kudin da za a ringa biya ba.

Sannan kuma Creators zasu samu dama ta switching Zuwa chat mode kawai, ga Wanda sukai subscription, da sauran wasu damanmaki da yawa na samun personal connection daga creator Zuwa masu kalla, inji Company TikTok.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!