WASU DAGA CIKIN FA’IDODIN AMFANIN DA HULBA TA KUNSA

Tafuskar magunguna,akan wasu cutuka. Domin idan akayi magana akan amfanin hulba, da kuma habbatusauda, to sai dai kace kasan wasu, domin baka gama iya sanin amfanin su, tun daga Wanda zaayi amfani dasu zallah da kuma wajen hada wasu magungunan muslunci, hakan kuma yabiyo bayan sakamakon abinda manzon Allah saw. Yafada akan wadannan itatuwa guda biyu.

(1)Ana maganin ulser da garin hulba, idan ake hada hulba cokali daya na hulba, cokali daya na zuma mara hadi asha, duk bayan awa 8.

(2)Tana taimakawa akan ciwan tari Mai tsanani wanda bayajin magani, ko yaki warkewa, da kuma bangaren matsalolin ciwan kunhu,ko asama inda zaa rika tafasa hulba, ko azuba arwan dumi abar shi minti 10-15 sannan asha, zaayi hakan sau uku arana.

(3)Hulba tana karama hanjin mutum karfi tafuskar narkar da abinci, da kuma sauki wajen tafiyar sa.

(4)Tana taimakawa mazaje wajen basu nishadi, da kuma karin kuzari, musamman tafuskar maza, idan andaka yayan habba, tare da yayan hulba sai azuba aruwan dumi ,abar shi minti 10-15 ko sama sannan asha indai sunada kya babu algush, kuma basu lalace ba kwana biyu zuwa uku ne zaka sakamakon aikin akan abinda nafada insha Allah.

(5)Hulba tana magance rashin bayan gida wanda yake faruwa sakamakon cin abinci mara tsafta, da sauran rashin bayan gida wanda wasu matsalolin suke haddasawa.

(6)Tana karfafa mahaifha, tare da nishadar ta da ita ga mata shi yasa mata kanyi amfani da ita awatan 9 domin samun sauki wajen haihuwa.Bayan haka wajen karbar haihuwa amfani da man zaitun yana saukaka wa, kuma yataimaka wajen haihuwa Lafiya, batare da mace tasamu Kari ba, koda kuwa haihuwar farko ce, wannan kam abune da aka jarraba, ko aka tabbatar insha Allah.

(7)Hulba tana saukaka radadi ciwan mahaifha, ko ciwan mara tahanyar dafata ana shiga cikin ruwan na mintina 10.
Bayan ahada hulba da habbatusauda da Kisdul hind anayin shayin sa tare da zuma ana sha.

(8)Hulba tana baiwa gool blader nishadi, tana Kara sinadari insulin acikin jini, wanda hakan akarshe zata iya saukaka ciwan suga ga masu fama da ciwan suga, zaa yi wannan ta hanyar shan cokali daya na garin hulba mai kya arana sau uku.

(9)Tana rage yawan kitse ajiki wanda yake karuwa, don haka akarshe idan ana sha zatayi reduced na cholostrol na cikin jini wanda yake cutar da jiki, tare da dagowa na cholostrol Mai amfani.

(10)Hulba tana Kara bubbgowa da ruwan no-no musamman ga mata masu shayarwa,shi yasa likitoci sukan bayar da shawara arika shan man hulba sau uku arana.

(11)Tana sanya fitar jinin alada musamman ga yan mata idan suna shan hulba karamin cokali sau biyu arana

(12)Hulba Mai kya tana da amfani sosai, kuma tana taimaka wa sosai ga mata wadanda suka haihu, to bayan haihuwa idan suna Shanta takan dawo masu da jinin da suka zubar wajen haihuwa,tahanyar Shanta sau uku arana.

(13)Mata idan suna shan hulba musamman wadanda suka haihu hulba tana rage hadarin kamuwa da ciwan kansa na no-no cikin yardar Allah, da kuma ikon sa.

(14)Hulba tana magance yawan fitsari idan aka haɗa cokali na hulba da cokali biyu na habba da zuma mara haɗi ana shan cokali ɗaya da safe kafin break fast,da kafin a kwanta barci idan akayi nasati ɗaya za’ayi mamaki insha Allah.

(15)Hulba tana kara girman nono ga mata idan aka shata tare da zuma mara haɗi,da kuma madara safe da yamma za’ayi na wasu kwanaki zaaga abin mamaki, Ko kuma ayi amfani da man nata mai kyau a shayi,ko a ruwan ɗumi,a sanya zuma a sanya madara.

(16)Hulba tana kara ruwan mama ga mata masu shayar wa idan suna shan garin ta a shayi,ko manta a shayi,amma susanya madara bayan haka su sanya zuma mara haɗi wannan zai taimaka wajen kara ruwan mama cikin gaggawa,da kuma gyara jikinki dana yaronki, kuma zata sanya yaronki kumari da kuma kiba amintatta!

Dafatan Allah yabamu dacewa Allahumma amen.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!