YADDA AKE FITAR DA RUWA IDAN YA SHIGA CIKIN WAYARKU TA HANYAR AMFANI DA WANNAN APPLICATION

Yadda Ake Fitar Da Ruwa Idan Ya Shiga Cikin Wayarka Ta Hanyar Amfani Da Wannan Application.

Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci sannunmu da sake jamewa daku a cikin wannan shafi namu mai tarin albarka Howgist.com

A cikin darasin namu nayau zamu kawo muku cikakken bayani akan yadda zakuyi maganin duk wata matsala ta datti ko ruwa idan ya shiga cikin wayoyinku na Android.

Misali zai iya kasancewa wayarka ta fada ruwa ko kura ta shiga cikinta wadda ta sanadin haka sai kaji speaker ta wayar ta daina kara ko kuma ruwa ya hanata yin kara.

To idan haka ta kasance sai kayi amfani da wannan application wurin kawar da wannan matsala cikin gaggawa

Yadd wannan application yake aiki shine da zarar kayi installing dinsa akan wayarka to zakayi open dinsa, daga nan zaka danna Eject Watar Now to daga nan zai fara wata kara kala kala.

Zai dinga fitar da ruwa ko kura daga kofofin da suke jikin wayartaka gaba daya zaka iya yi kamar sau biyu ko uku domin fitar da duk wani ruwa ko kura daga cikin wayarka.

Amma gudu ba hanzari ba kamar yadda kuka gani a tubuce anfi amfani da wannan application ne a yayin da wayarka ta fada ruwa.

Ba,a fiya amfani dashi domin fidda kura daga cikin wayaba, wannan dai shine takaitaccen bayani dangane da wannan application wanda anan gaba kadan zamu ajiye muku link nasa domin kusamu saukin download nasa akanwayoyinku.

Ga link dinsa nan a kasa saiku danna wurin da aka rubuta download now domin saukeshi cikin sauki batare da wata wahala ba.

Idan kuma wannan baiyi akan wayarkaba, to zaka iya duba sunansa bayan kayi download saika hau kan google playstore ko google akan wayarka ka rubuta sunansa domin daukowa wanda zaiyi dai dai da wayarka.

Download Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!