YADDA UWARGIDA ZATA HADA MAN KWAKWA ORIGINAL DA KUAMA ANFANONINSA
ammfanin man Kwakwa wajen warkar da wasu matsalolin da ke damun mata, wadanda suka hada da rage tumbi da warkar da nankarwa, wato ‘Stretch mark’ a Turance
A kan samar da danyen man kwakwa ba tare da kona wani abu daga amfaninshi ba. Ba shi da wahalar hadawa, ba a bukatar yin amfani da wuta, kamar yadda na fada a baya
Da farko, uwargida za ta samu kwakwa daidai bukata, sai ta cire bawonsa, ta yayyanka su kanana, sannan ta markade sosai. Bayan kin markade, sai ki gtace ruwan, ki dura a roba, sannan ki ajiye shi a wuri mai iska, ki bar shi ya kwana
Da safe za ki ga mai ya taso a sama, ki sa cokali, ki yade man, ruwan ne kadai zai rage a kasa. Za ki gan shi kamar man shanu, in kuma kina bukata, kafin ki yade man, sai ki saka shi cikin firji don ya yi kankara. Hakan ya fi dadin yadewa, za ki gan shi kamar man kade
Masana sun tabbatar cewa ya fi dafaffen man kwakwan tasiri
An nuna cewa za a iya shan shi haka nan domin rage tumbi. Baya ga wannan, za a iya amfani da shi wajen magance Amosanin kai, wato ‘Dandruff,’ don haka za a iya amfani da shi a matsayin sinadarin wanke kai (Shampoo). Ko kuma a hada shi da man kitso da man shafawa domin gyaran jiki matuka
Ta bangaren warkar da nankarwa kuwa, babu kamar man kwawa. Da zaran kika fara amfani da shi wajen shafawa a jikinki, tabbas za ki nankarwa ta fara bacewa
Don haka a takaice kwakwa da manta suna da matukar amfani ga mace, baicin wadannan da muka lissafa. Ruwan na magance wasu cututtukan jiki, musamman masu cututtuka a mafitsara, wanda ake kira a Turance ;Urinary infections.