GYARAN TAFIN KAFA DON KAUCEWA FASAU LOKACIN SANYI

‘Yan’uwana mata yanzu zan yi bayyani ne a kan yanda za mu kula da tafin kafanmu, ba ku ba zuwa wajen wanke kafa, kawai za ku yi amfani da wannan hadin kuma za ku ga abin mamaki. Ga ababen da za
ku tanada:

  • Man shanu
  • Man kwakwa
  • Man ridi
  • Man alayyadi

Zaku hade wanan mayukan gu daya, idan kafa tana
tsagewa ko tana kaushi, da daddare idan za ki
kwanta bacci sai ku shafa wannan mayukan a tafin
kafarku sai ku sami leda ku daure kafar da shi ku
kuma saka safa (socks) da safe ku wanke kafar da
ruwan dumi ku shafa man zaitun da man ridi. Ko
kuma ku nemi

  • Man kwakwa
  • Man shanu
  • Man zaitun

Sai ku hade su gudaya suma kuringa shafawa da dare kuma saka leda kuna daure kafar sannan kusa sake safa (socks) idan gari ya waye ki fara gasa kafar kadan sannan ki wanke da ruwan dumi, ki shafa masa man zaitun.
Wannan hadin wanke kafa ne sai a tanadi:

  • Kokumba
  • Halle
  • Man ridi

Sai ku tanadi ‘Cucumber’ ku fere bayan ku yanyanka shi kanana, a markada, amma fa kar a cika masa ruwa domin an fi son ainihin ruwan ‘Cucumber’ din sai a kwaba lallen da ruwan cucumber din, a rika amfani da shi da dare, ana cirewa a wanke da safe,
ku kuma wanke kafar da ruwan dumi sai a shafawa kafar man ridi insha Allah, indai aka rike wannan hade-haden, za a ga amfaninsa, kuma za a yi mamakin irin kyan da tafin kafar ku zai yi. Allah ya taimakemu

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!