Yadda Za ki Kare Kanki Daga Ciwon Sanyi (Toilet Infection)

Mutane da yawa, musamman mata, suna fama da yawan fitar da ruwa daga al’aurarsu. Wannan fitar ruwan yana iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ko rashin lafiya ba. Mata sun fi yawan samun kansu a wannan yanayi na fitar ruwa daga mafitsararsu fiye da maza.
Wannan bayanin da zan yi, zan fi karkata a kan mata.
Yanayin yadda Allah (SWT) ya yi cikin al’aurar mace shi ne, ya kasance a jiƙe (mai danshi-danshi) a kowane lokaci.
Ruwan da yake jiƙa a gaban mace yana fitawo ne daga wasu ɓangarori daban-daban da suke cikin gaban nata. Yawan ruwa yana iya ƙaruwa, raguwa ko kuma yana ɗauke gaba ɗaya. Zan yi bayani a kan ƙaruwar ruwa.
Wannan zubar ruwa ana kiransa “vaginal discharge” a likitance. Hausawa suna kiransa da “ciwon sanyi”, wasu kuma suna kiransa da “toilet infection (ma’ana, cutar da ake ɗauka a banɗaki maras tsafta)”. Ya kamata a sani cewa, har yanzu, a likitance, ba a tabbatar da cewa yin amfani da banɗaki marar tsafta yana ɗaya daga cikin hanyar da ake kamuwa da wannan cutar zubar da ruwan ba, amma dai ana zargin hakan, kuma ya kamata a yawaita tsaftace banɗaki.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!