Yadda Zaka Dora Account Number Ka Bayan Kayi Screening Na Aikin Kidaya
Jama’a Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Kamar de yadda kuka sani tuni de hukumar kidaya ta fara screening bayan sakin jerin sunayen wadanda suka cika a kowace karamar hukuma, tare da sakin PDF na kusan kowane gari.
Tu ni de akayi Nisa da fara screening domin kuwa wasu daga cikin wadanda sukayi screening har sun dora account number su.
Sai de kuma har yanzu akwai wadanda basuyi screening ba sakamakon sun rasa Application ID din nasu.
Dan haka duk wanda ya Rasa application id nasa ya shiga Link dinnan dake kasa domin dubawa 👇
Yadda Zaka gano Application ID dinka
Bayan ka gano application id dinka sai kaje inda ake screening din a garinku domin ayi maka screening.
Bayan kayi screening kamar da kwana biyu to yanzu ga yadda zaka dora account number ka wato bank details dinka.
Da farko zaka shiga wannan Link din
https://doanncx4d1b7d.cloudfront.net/
Idan ya bude saika shiga Check Application Status saika sanya Application ID dinka, daga nan saika Danna Proceed, da zarar ka danna zai kawo maka sunanka da kuma App id dinka sanna daga kasa zakaga Approved, sannan daga kasansa zakaga Submit Bank saika danna ka shigar da sunan bankin ka da account number ka.
Idan kuma ka shiga kaga Pending, to karka damu ka sake jira daga baya zakaga approved insha Allah.
Allah ya bada sa’a