yadda zaku bude message din ya’yan ku ta Cikin wayarku ba tare da sun sani ba

Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da sake saduwa da ku a cikin wannan sabon darasi a yau nazo muku da wani Website mai matukar amfani wanda na tabbata zai burgeku.

YANDA ZAKA BUDE MESSAGES DIN WAYAR BUDURWARKA A WAYARKA 

wannan wani sabon website ne mai suna (message for web) zai baka dama ka dinga ganin dukkan nin message wanda aka turawa budurwarka da message din data tura ta cikin wayarka ba tare data sani ba cikin sauki.

Iyaye maza da iyaye mata zasu iya amfani da wannan muhimmin Application din domin kula da tarbiyyar ya’yan su kuma susan da wanne irin mutum ya’yan su suke mu’amala mutumin kirki ne ko mutumin banza musamman ga yan mata kula da tarbiyyar yara ba iya a hannu iyaye take hatta kai idan ka kasance babba ne a gida kuma kana da kanne maza da mata to kaima ya wajaba ka dinga kula tarbiyyar kannen nan naka.

zaku iya amfani da wannan website din wajan ganin kalar message din da ya’yan ku suke turawa da kuma wanda ake tura musu wannan babbar hanya da zaka iya gano abin da yarka ko danka ko kanwarka ko kaninka ko wani dan uwanka suke boyewa idan abun ne da za’a iya tsawatar musu a tsawatar musu idan kuma nasiha ce ayi musu nasiha.

HANYOYIN DA ZAKA BI WAJAN BUDE MESSAGE DIN WAYAR BUDURWARKA TA CIKIN WAYARKA 

Da farko zaka karbi wayar wanda kake so ka dinga ganin dukkan nin message din da ake turoma da message din da yake turawa kana karbar waya zaka shiga Application na message dake wayarsa kana shiga daga barin hannun damar ka daka sama zakaga wani layi layi guda uku zaka danna shi kana danna wa zakaga ya kawo ma rubutu da yawa a cikin rubututti kan zakaga inda akasa (message for web) saika danna kana dawa zai kawoma (QR Code scaner) saika danna ka shiga kana shiga zai kawo ma CAMERA wanda ake Scanning din CODE da ita.

Kai kuma wanda kakeso ka dinga ganin ko wanne kalar message a wayarka zaka nemi Browser da kake amfani da ita saika shiga kana shiga zaka danna alamar Searching kana danna wa zaka rubuta (message) kana rubutawa zaiyi Searching bayan ya gama Searching zai kowama website da yawa saika duba can kasa zakaga inda akasa

(message for web message Google) saika danna kana danna wa zai kawo ma Code wanda ake scanning dinsa tare da wata alama wacce ake budewa da rufewa zaka ganata a rufe saika bude ta kana bude ta idan baka manta ba a waya wanda kake so ka dinga ganin dukkan nin message din da ake turoma sa da message din da yake turawa mun shiga wajan App na message dake wayarsa ya bayyana mana alamar scanning wacce ake scanning din Code to kai tsaye zaka dauki wayar kayi scanning din wannan code din dake wayarka kana yin haka to shikenan zaka dinga ganin dukkan nin message din da aka tura da wannan wayar da kuma message din daka turo cikin ta.

zaka dinga ganin dukkan nin wannan message din ta cikin browser da kayi amfani da ita wajan Searching din wannan code din sannan zaka iya yin futowa daga cikin browser anjima ka koma ba tare da wannan setting din hargitse ba.

KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

mungode 🤝🤝🤝

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!