Yadda Zaku Bude Profile Na JAMB/UTME 2023 Tundaga Yanzu

UTME 2023 : ZA KU IYA FARA BUƊE PROFILE DAGA YANZU.

A shirye-shiryen ta, na tunkarar jarrabawar JAMB UTME ta shekarar 2023, hukumar JAMB ta bayyana cewar ɗalibai za su iya ƙirƙirar Profile Codes ɗin su tun daga yanzu, su kuma adana shi, domin yin amfani da shi a lokacin da aka fara rijista.

Hukumar JAMB ta bayyana hakan ne, ta cikin mujallarta ta mako-mako da ta saba fitarwa, a duk ranar Litinin, a babban birnin tarayya Abuja.

Inda hukumar ta ce, hakan na daga cikin matakan da ta ke ɗauka, dan tabbatar da gabatar da rijistar UTME ta shekarar 2023 lami-lau, ta hanyar kakkaɓe dukkannin wata ɓaraka, da matsaloli.

√• YADDA ZA KU ƘIRƘIRI PROFILE CODES :

• Ku shiga wurin rubuta saƙon kar ta kwana na wayoyin ku (Messages), sai ku rubuta : NIN, ku kuma bada tazara, sannan ku rubuta lambobin katin ɗan ƙasar ku guda 11.

Misali : NIN 12345678901.

•Sannan sai ku aike da saƙon zuwa 55019, ko 66019.

Daga nan, hukumar ta JAMB za ta aike mu ku da saƙon wasu lambobi guda 10, sai ku samu takarda ku rubuta su, ku kuma adana.

KU SANI : Wannan tsarin ya shafi dukkannin ɗaliban UTME da DE.

Allah yataimaka aamin

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!