YADDA ZAKU FARA SAMUN KUDI A INTERNET DARASI NA BIYU (2)

Barkan mu da sake kasancewa daku a darasi na biyu 2

Assalamu Alaikum warahamatullahi ta’ala wabarakatuhu ‘yan uwa barkan mu da wannan lokaci sannun mu kuma da sake kasancewa daku a yau a darasin koyon samun kudi a internet darasi na biyu (2), wanda a baya munyi darasi na farko wanda bai karanta darasi na farko ba yadanna nan domin karanta darasin farko.

DANNA NAN DON KARANTA POSTING DIN FARKO

To kamar yadda mukayi alkawarin kawo darasi na biyu(2) ina fata kowa yana tare damu a yanzu domin kara sauraren wasu muhimman abubuwa da zasu kara taimakawa mutum wajen samun kudade a internet ta yadda har zaina iya dogara da kansa, wasuma sukaru dashi yakaru dasu.

A darasin mu na farko munkawo abubuwa da dama wadanda ake amfani dasu wajen samun kudi a internet ina fata mutane sun amfana da wadannan hanyoyi kuma sun fara amfani da wasu daga cikin su.

To yau zamu kawo wasu shawarwari da zasu kara taimakawa mutum wajen kara bunkasa harkokin kasuwancin sa ko harkokin sana’ar sa a internet, domin ya karajin karsashi da zummar kara dagewa akan sana’arsa da yasa agaba.

Karna cikamu da surutu bara muje ga gundarin bayanin daya kawo mu, duk da yau rubutun namu zai danyi tsayi sai an danyi hakurin juriyar karantawa.

Wato kasuwancin yanar gizo kamar yadda muka sani yanada ma’anoni daban-daban don haka wasu sukan cire rai a yin amfani da shi wajen faɗaɗa kasuwancinsu na zahiri ko kuma fara wani sabo. To amma maganar gaskiya shi ne yanada sauƙi matuƙa. Matukar dai za ka jure da ƙalubalen da za ka iya fuskanta ko wata wahalar da za ka sha, in Allah ya yarda kai ne da riba a karshe, domin ance wanda yayi hakuri shine zai dafa dutse har yasha roman sa.

Kasuwancin yanar gizo ko muce internet ya danganta da irin wanda kaga ya dace da kai ka dauka kakeyi, kowa da irin nasa kasuwancin a internet kowa da wanda yake ganin ya dace dashi yake ganin yanada fahimta akan abin ya dauka.

Dan haka ga raba raben wasu hanyoyin bayan wadanda muka kawo a darasin farko wadanda ake amfani dasu wajen samun kudi a internet suma zakui iya amfani wasu wajen nemowa ‘yan canjinan ku

(1). Kasuwancin saye da sayarwa – wanda mutum yake sayen kaya shi ma yaje ya sayar don samun riba.

Irin wannan kasuwancin shi ya fi yawa, saboda ana ganin yadda mutane suke tallata hajojinsu a media da sauran wurare a internet.

A gaskiya irin wannan kasuwancin yana da riba sosai, wato dai ya fi sauki matukar kanada abun farawa, domin ba ya bukatar kashe wasu makudan kudade.

Zamuzo da rababen kasuwancin saye-da-sayarwar internet dama yadda akeyin su a darasi na gaba insha Allah.

(2). Aikin ƙwadago

Nasan mutum zaiyi mamaki yaji munce aikin kwadago, zai tambaya..??, to tayaya mutum zaiyi aikin kwadago a internet, wasu kuma bama susan me ake kira da kwadago ba a zahirance ma balle a Internet to yanzu duka kowa zamu warware masa me ake nufi da kwadagon a zahirancen da kuma internet.

ƙwadago shi ne wani aiki da za kayi a biya ka, tunda ana zamanantar da abubuwa, misali yadda za ka yi leburanci a zahiri kaje kayi aiki a biyaka a take kamar kaje kayi dako a biyaka a take, to shi ne irin wannan aikin ƙwadagon amma dai shi aikin kwadago na yanar gizo ya sha bamban da wancan na zahiri, shima zamu fayyace yadda yake da yadda akeyin sa a darasi na gaba.

(3). Kasuwancin kamasho

Misali zan ce ka nemo min kwastomomi su sayi kayana, duk wanda ya saya zan ba ka wani percentage a ciki.

Ka ga ke nan ba sai lallai a rayuwa ta zahiri yake faruwa ba,

bara na bamu misali aka yadda yake a zahiri shima,

za kaga ma’aikacin NURTW, wato ma’aikatan da suke kula da motoci a tasha, zakaga ma’aikacin NURTW, yaje ya nemowa mai mota parcengers su hau motarsa shikuma yabawa ma’aikacin wani abu.

Wannan shi ake kira da kamasho a zahirance shima na internet kusan hakan yake sai dai akwai dan banbanci kadan dana internet, domin shi na internet kana kwance a ɗaki amma kana samun fiye da yadda kake tunani ma, Shima zamu kawo muku hanyoyi yadda akeyin kasuwancin kamasho a internet a darasi na gaba.

Alhamdulillah anan zamu dakata saboda kada rubutun namu yayi tsayi insha Allah a darasi na gaba zamu kawo raba-raben yadda akeyin kowanne kasuwanci daga cikin su.

Muna fata kuna amfana da abubuwan da muke kawo muku.

Dan Allah kada kumanta wajen yin share na rubutun mu domin ‘yan uwa su shigo su karanta suma su amfana.

Mungode sai mun hadu daku a darasi na uku.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!