Yadda Zaku Hana Wanda Bashi Da Number Ka Ya Kiraka Video Call ko Voice Call A Whatsapp

Assalamu alaikum barkanmu da wanann lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya

A yau zanyi muku bayani akan yadda zaku hana wani wanda baida save na number ku ya kiraku video call ko voice call a whatsapp.

Kamar yadda kuka sani whatsapp ya bada damar duk wanda yake da number ku koda baku da number sa zai iya kiranku a whatsapp video call kokuma voice call.

Hakan yana bawa mutane matsala musamman mata, domin baka ko baki da number wani sai kawai a kiraka video call.

Idan kabi wanann hanyar zaka maganace wannan matsala domin kuwa duk wanda ya kiraka kiran bazai shigo ba kokuma nace baza kaga kiranba har sai inka shiga wajen history na kiran sannan zaka gani.

Da farko ka kayi Update na whatsapp dinka kaje playstore sai kayi search dinsa sai kayi update idan kuma already kayi update shikkenan.

Bayan kayi Update saika bude shi kanshiga cikinsa saika shiga wanann … Na sama,

sai ka shiga Settings

Daga nan saika shiga Privacy

Saika shiga kayi can kasa ka zabi Calls

Zaka ganshi a off saika kunna Shi.

Da kayi haka shikkenan duk sanda wanda baka da number sa ya kuraka kiran bazai shiga ba, amma idan ka duba wajen kiran zaka gani.

Ga Video na yadda zakayi

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!