Yanda ake shiga Email wato na Gmail cikin sauki

Email yakan bamu damar tura abubuwa da dama kama daga rubutaccen sako, sauti, hoto da kuma hoto mai mosti cikin sauki zuwaga abokan hulda ko kuma abokan arziki. A makon daya gabata nayi cikakkiyar bayani dalla dalla ma’anar sa da kuma yadda ake bude shi tare dashi gmail. A wannan karon kuma insha Allahu zan nuna muku hanyar da ake bi wajen shiga account na gmail din da aka bude.

Matakin Farko: Mutum zai ziyarchi addreshin gmail din wato www.gmail.com zai kaisa izuwa ga shafin nan wanda shine babban shafinsu na shi gmail.
A sama can bangaren hannun dama mutum zaiga inda aka rubuta “Sign in” wanda ma’anar sa a hausance shiga ciki. ba lallai bane mutum yaga wannan shafin mafi yawancin lokutan yana kai mutum ne izuwa ga mataki na biyu koda yake ya dan ganane da wani irin browser mutum yake aiki dashi ko kuma wani irin salula mutum ke aiki dashi a mafi akasarin lokutan yana nunawane wa masu aiki da chrome browser ko kuma masu aiki da kwanfuta.

Mataki na Biyu: za’a umurci mutum yasaka email nasa a dan akwatin dake k’asan nan sai na sanya shi a cikin akwatin tare da latsa ma bullin “Next”

wanda zai bada damar zuwa mataki nagaba. Akwai wasu sa’in da zai rubuta wa mutum “Email not found” kodai maka mancin haka yana gayawa mutum cewar email daya sanyan nan ba dai dai bane wata kila an yi tuntuben kalma wajen rubutu dole mutum ya lura a lokacin da yake rubutawa dan gujewa kuskure.

Mataki na Uku: Zai tambayi mutum ya sanya numbobin sirri wato wanda aka fi sani da password a turance, sai mutum ya sanya shi tare da latsa mabullin “Next”

in dai mutum ya sanya numbobin sirrinsa daidai zai kaisa izuwa ga account nasa in kuma ba dai dai bane zai fito da wani rubuta mai kala ja dauke da “incorrect password” ko kuma “wrong password” koma wanne ya sanya maka daga ciki yana gaya maka cewar numbobin sirrin ba daidai bane sai ka goge su sannan ka canza zuwa wani wanda ka sanya a lokacin da kake budewa.

Wannan shine cikkakiyar hanya da ake bi wajen shigan email naka na gmail ku

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!