ABUBUWAN KWALLIYA DA FATA KE BUKATA
Sakamakon irin nau’ukan man shafawa na zamani wanda mata da dama basu san dame ake hada su ba. Su dai daga ganin ya yi kyau sai ace zai wa fata kyau. Yawan shafa irin wadannan na’ukan man na haifar da kuraje wadanda ba su saurin barin fuska. Koda kuwa sun bar fuska sai aga tabon na nan baya bata. Don haka ne a yau na kawo muku abubuwan kwalliya shida wanda ko a gida za’a iya hadasu domin samin fata mai laushi kuma mara kuraje.
• Man zaitun; yana dauke da sina daren rage maiko a fuska. Don haka yana da kyau idan za’a sake yin kwalliya a sami auduga a tsoma a man zaitun a rika goge fuskar da ita kafin a sake maka wata kwalliyar. Yin haka na hana fesowar kuraje a fuska.
• Kwakwa; sai aga mace fara kyakykyawa kamar a wanke hannu kafin a taba amma daga an taba hannunta sai aji shi kamar tana faskare da surfe tsabagen tauri. Idan ana da irin wannan matsalar, sai a sami kwa-kwa a kankare bayansa sannan a markada da ruwa kadan a tace sannan a sanya a firiji. Idan ta yi sanyi sosai sai a rika shafawa a tafin hannu yana sanya fatar hannu laushi.
• Zuma da siga; idan mutum na fama da fata mai yawan saba musamman ma fatar fuska, sai a hada zuma da siga a guri guda sannan sai ya shafa a fuska na tsawon mintuna talatin kafin a a murza a fuska. Yin hakan na cire fatar da ta mace a fuska domin bawa sabbin fata waje. Idan an gama sai a wanke da ruwan dumi.
• Madara/kindirmo; yana sanya fatar fuska laushi da santsi. A sami madarar kindirmo sannan a shafa a fuska na tsawon mintuna talatin a kullum kafin a kwanta bacci. Yin hakan na kashe kowace irin kwayar cutar da take fesowa a fuska ko kuma a fata.
• Kwai; a sami ruwan kwai a cire kwaiduwar sannan a rika bugawa har sai ya yi kumfa. A shafa a gashin kai na tsawon awa daya ko rabin awa sannan a wanke da man wanke gashi. Yin hakan na cire dattin dake cikin gashi da kuma hana gashi karyewa.
• Fiya; shima yana gyara gashi sosai. A kwaba ta tayi laushi sannan a shafa a fatar kai domin hana futuwar amosanin ka. A bari a fatar kai na tsawon mintuna talatin kamin a wanke da ruwan dumi.