AMFANI 5 DA CUCUMBER YAKEYI A JIKIN DAN ADAM

Gurji wanda aka fi sani da Cucumber a turance, wani nau’in kayan abinci ne da ke taimakawa wajen saukaka sarrafa abubuwa masu tarin yawa a jikin dan Adam.

Yana dauke da sinadarin ‘Vitamin C’ da ‘Caffeic acid’ wadanda suke taimakawa wajen gyara fatar jiki.

Ga biyar daga cikin amfaninsa a jikin dan Adam:

  1. Narka abinci cikin sauki: Cucumber na taimakawa wajen narka abincin da mutum ya ci cikin sauki. Yana kuma taimaka wajen kara garkuwar jiki daga kamuwa da cututtuka.
  2. Rage kiba: Cucumber na dauke da sinadarin ‘fibre’ wanda yake taimaka wajen rage ko hana yin kiba.
  3. Daidaita ruwan jikin dan Adam: Kashi 96 cikin 100 na cucumber ruwa ne, wanda hakan ke taimaka wa jikin mutum wajen fitar da abu mara amfani daga jikinsa cikin sauki.
  4. Warin baki: Wani amfani da cucumber shi ne maganin warin baki. A wasu lokutan mutum na samun warin baki sakamakon wata cuta ko abinci da ya ci, amma cucumber na iya maganin hakan cikin sauki.
  5. Kariya daga cututtuka: Cucumber na dauke da ‘antioxidants’ inda yake taimaka wa gangar jiki wajen yakar duk wata cuta da ta shiga jikin mutum a matakin farko.

Cucumber na da amfani mai tarin yawa a jikin mutum, don haka yake da kyau mutane su rika amfani da ita don su amfana.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!