ANFANIN TAFARNUWA GA LAFIYAR JIKI DAYA KAMATA KU SANI
Shekaru dubbai da suka shude mutanen kasar masar ke amfani da tafarnuwa don gudanar da magungunan matsalolin jiki dabam-dabam. Har ya zuwa wannan zamani da masana suka gudanar da bincike na zamani don tabbatar da irin alfanunta ga lafiyar dan-adam.
Binciken zamanin ya tabbatar da cewa ita tafarnuwa na gyara hanyoyin jini, kuma mun bayyana a sama yadda gudanuwar jini ke da alaka da mikewar gaban namiji. Hakanan tana gyara zuciya wadda itama an san aikinta na wajen tunkuda jini cikin jiki. Don haka wannan na bayuwa zuwa ga karfin al’aura yayin jima’i,sa’nan tafarnuwa na Kara lafiyar jiki don haka Al’umma kada ayi wasa da tafarnuwa kwarai da gaske .