ANYA MATAR NAN TA KYAUTA KUWA ?

AMMAN SHIMAFA ƊAN SON BANZA NE.

SHIYASAH AKACE INZAKA GINA RAMIN MUGUNTA GINA SHI GAJERE.

AMMAN FA DUK DA HAKAN BANA GOYON BAYAN ABIN DA ƳAR ALJANNA TAYI

Jiya bayan na fita kasuwa sai kawai naga Mai Dakina ta min magana a WhatsApp

Abban Sultan yau kaji da kifi muke bukata a gidan.

Nace toh kuci mana.

Sai tace zaka aiko dasu yanzu ko mu saya anan.

Nace ku saya anan din. .tace guda nawa kajinTarwadar kuma kilo nawa

Cikin gatse nace mata kaji 10 tarwada kilo 5

Tace wow ta tura wasu stickers.

Toh ni dai nasan ban ajiye ko sisi a gidan ba iyaka dai in ta saya da kudinta sai ta dora akan bashin da ake kakaba min na babu gaira babu dalili

Kuma nama san ba zata iya sayen adadin da nayi mata gatse ba. Karkari tayi kuru ta sayi kowanne guda dai dai..

Kuma na kudurce a raina in ta saya bazan biya ba.

Kawai na sauka daga WhatsApp na kashe data ma dan kar muyi dogon zance.

Ga mamakina ina dawowa naga an gama gyara komai kamar yanda na ambata an soya na soyawa anyi farfesun wasu wasu anyi miyi saura kuma ansa a FIRIZA

A Raina nace zanci banza kenan Dan wlh ba biya zanyi ba.

Na dauki wayata na kira abokina nace kar kaci komai fa yau kazo gidana yar Aljanna ta shirya mana liyafa.

Na kalleta cikin murmushin keta nace ina zobo. Tace ai aiki ne yayi yawa amma na siyo five alive.

Nace wohoho Allah ya baki Aljanna tace Ameen.

Bayan naje sallar Magariba sai nace bari in biya gidan su amaryar can in karbo kudin ankon dana fidda musu. Makociyar mu ce bikinta za’ai kuma ni na fidda ankon nata

Akwai kudin turmi 10 da zata bani dama.

Ina biyawa nayi sa’a kuwa ta dawo daga rabon goro nace mata amarsu miko inyi gaba.

Tace me fa nace 45k

tace auho

Baka koma gida bane nace daga gidan nake naje sallar Magariba ne sai na biyo tanan

Tace okay ai tun safe na shiga tace yanzun nan ka fita kasuwa sai na bata kudin.

In kaine Ya Zakayi?

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!