DAUKAR AIKI: Gwamnatin Jihar Borno ta Bude Shafin yanar gizon daukar Malaman makaranta 30,000 a fadin jihar

Gwamnatin Jihar Borno, ta bude shafin yanar gizo da za a yi amfani da shi don neman gurbin aikin sabbin malaman makaranta 30,000 da za ta dauka

Sanarwar da ta fito ta hannun Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Ali Musa, ta bukaci masu sha’awar aikin kuma suka cancanta, da su je su shigar da bayanansu ta wannan adireshin na yanar gizon http://moeapplication.bornostate.gov.ng

Daga cikin sharuddan cancantar neman aikin kamar yadda sanarwar ta nuna, ban da wadanda suka haura shekara 50 da haihuwa.

Sanarwar ta ce za a rufe shafin neman aikin ne ya zuwa 31 ga Disamba, 2022.

Gwamnatin Borno, karkashin Gwamna Babagana Zulum, ta dauki matakin daukar sabbin malaman ne domin inganta fannin ilimin jihar.

Apply now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!