GYARAN FUSKA DA MAGANIN KURAJEN FUSKA

Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu insha Allah yau zaku koyi yanda ake amfani da kwai wajen magance kurajen fuska, a hakikanin gaskiya kurajen fuska na daya daga cikin ababen da ke bata fuska. Akwai wadansu kuraje masu yawan naci. Ya kamata mu kula da fuskarmu musamman ma lokacin damina saboda a lokacin ne fuska takan fitar da gishiri watau a Turance ‘sebum’, kamar yadda muka sani, gishirin fuska na toshe ramukan da gumi ke fitowa. Idan hakan ya faru, sai fuska ta fara yin kuraje.

Ababen da za a bukata:

Kwanuka biyu
kwai daya
Takardar ‘tissue’ daya

Amfanin kwai ga fuska:
· Ruwan kwai na da sinadarin gina jiki da sinadarin bitamin da kuma ‘minerals’
· Yana kare fuska daga kuraje.
· Yana kuma rage tsufar fuska.
· kara wa fuska haske.
· Rage kumburin ido.

A samu kwano daya sai a zuba ruwan zafi, wanda da shi ne za a turara fuskar. Kwano na biyu kuma sai a zuba ruwan kwai bayan an cire gwaiduwar, sannan a shafa ruwan ‘rose water’ saboda samun biyan bukata.

Hadi:
A fasa kwai sai a cire gwaiduwar. A kada farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa. Daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.

A yagi takardar ‘tissue paper’ kadan, sai a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu. A kara dora wata takardar ‘tissue paper’ a kan wanda aka manna a fuska tun a farko, watau hawa biyu kenan? Kada a yi dariya ko magana bayan an gama manna takardar ‘tissue paper’, domin yin hakan zai iya bude fuska, wadda kuma ana sanya takardar tissue paper din ne don ya matse fuska. Bayan hadin ya bushe, sai a wanke fuskar. Sannan sai a shafa gwaiduwar kwan a fuska na tsawon minti 15, sannan a wanke.

Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza. Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa. Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.
Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.
A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne.

· A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.
· Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.
· A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.
· a hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.
· A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!