HADIN DA YA KAMATA MACEN DA TA SAMU QARI WAJEN HAIHUWA TAYI

Abubuwan da ya kamata Macen da ta samu qari(budewa) wajen haihuwa tayi.

Musamman wannan matsalar anfi samunta a haihuwa farko to ya kamata duk matar da ta sami wannan matsala to tayi kokari ta gyara jikinta, domin karki cuci kanki. Abinda zaki nemo shine;

  • Bagaruwa
  • Hulba

Ki tafasa su in yayi dai-dai shiga sai ki shiga haka zaki dinga yi to insha Allah zaki ga jikinki ya hade. Zaki iya hadawa da Ganyen magarya, Amma kar kiyi amfani da Alimun da yana lalata gaban Mace.

Wannan hadin ma Yana maganin matsalar budewar gaba,

Duk matar da gabanta ya bude amma ba ta San yarda zata yi ya koma ba, to ga dama ta sami yar’uwa ita dai wannan hanya tana da yawa, amma ga wata hanya da zaki bi mafi sauki

Ki tafasa Sassaken Bagaruwa, ko Bagaruwan kanta sai ki matsa lemon tsami dan kadan a ciki ki dinga zama zai hade ya koma dai-dai Insha Allah.

Sai Kuma ki samu kici Kazar Mai Jego, idan kikai haka to kin wuce wajen In shaa Allah, Allah Ya sa a dace, masu ciki Allah Ya saukesu Lafiya.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!