MAGUNNAN DA AKE YI DA MAN/QWALLON DARBEJIYA

Darbejiya wata bishiyace mai tsawo tana da manyan rassa da sayyu masu tafiya a cikin kasa da ganye launin kore da kuma ‘ya’ya kanani launin dorowa idan suka kosa,to a nan muna magana kacokam kan amfanin ‘ya’yan.

Man darbejiya na warkarda kusan kashi 70 na cutukkan fata kamar su

  • makero
  • Cin ruwa
  • garjen giwa
  • kaikayin fata
  • kazuwa

kuraje a sanadin cizon wasu kwari.

man darbejiya na lausasa fatar data bushe.Mai neman fatar jikinsa tayi laushe ya jarraba ya gani.zai yi mamaki.

Man darbejiya na warkarda kunan rana dake 6ata fuska inda zaka ga mutum fari da shi amma fuskarsa baka.ko yana baki amma fuskar tashi tafi fatar jikinsa dushewa.

Man darbejiya na warkarda kuraje masu kaikayi a kan fata da ake ta’allakawa da fungal infection.

Man darbejiya na kare fatar jiki daga kwayoyin cuta iri iri.
A gauraya da Vaseline a zanka shafawa.

Man darbejiya na maganin kefsi.

man darbejiya na maganin pimples da suka mamaye fuskar mace ko namiji.

Mai ne mai inganci musamman ta 6angaren gyaran gashi domin yana rina gashi yana kashe kwayoyin cuta dake lailayi a cikin kai musamman ga mata masu jin kaikayi ko wasu kuraje dake tsira a cikin fatar kai masu kaikayi ko zafi.

Man darbejiya yana warkarda tsagewar fatar jiki da bushewarta da garjin fata dama dushewar fata.

Man darbejiya na maganin cutukkan baki(mouth infections) kamar wanda ke brush yana ganin jini a hakoransa ko wanda dasashin sa ke kumbura yana masa ciwo.

Man diyan darbejiya yana maganin keyar kai musamman ga mata.
Sai a banye kai a saka sabulu a wanke da ruwan dumi a nemi man darbejiya original a shafa a shace da kyau washe gari za a ga yanda keyar zata mutu.

Man diyan darbejiya na maganin kunar fata a sanadin wuta.

Man diyan darbejiya na maganin dandruff ga maza da mata.

Man diyan darbejiya na maganin kurajen nan da ake kira na damina.

Man diyan darbejiya na maganin cutukkan ciki sai a nemi mai kyau a zanka shan 5ml a kullum za a ji banbanci a jiki.

Man diyan darbejiya na maganin kaikayin matse matsi a shafa kullum sau biyu.

Yana maganin ciwon daji kamar na mamma breast cancer da skin cancer.

Idan za a nemi man diyan darbejiya to a nemi original yana da launin dorowa da kuma kamshi kamar na tafarnuwa.
Akoi made in Mumbai India ko Jakarta a Indonosia da kuma Made in Egypt.Duka da kamfanin Hemani.

A kula akoi na yan kasuwa.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!