Hanyoyin da mace mai ciki zatabi domin zama cikin koshin lafiya

Idan mace tayi ciki yaron da yake cikinta yana zukan jininta sabida shine abincinsa wannan dalilin yasa mata masu ciki suna yawan samun karancin jini .
Yakamata ta samu nau’in abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki, kayan lambu, da kuma kayan mar-mari

  • Wake
  • kifi
  • Nama
  • kwai da sauransu
  • Dakuma ganye da kayan itatuwa kamar su
  • Salat
  • kabeji
  • Alayyafo
  • zogole
  • Lemu
  • kankana
  • Apple dasauransu .

Wanda cin abinci lafiyayya yana karawa mata jini , lafiya , yana karawa yaron da yake cikib ta lafiya da kaifin basira .
Rayuwar yau da kullum na mai ciki dole ya banbanta da na sauran mutane.

mace mai juna biyu baikamata tadinga aikin wahala sosai ba , yakamata tadinga hutu ko wacce rana .

idan mace mai ciki bata da lafiya dole taje asibity domin gudun kada tayi amfani da maganin da zai zama mata matsala ,ko zai yakawo matsaka ga yaron cikinta .

tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka .

maccen da take yawan amai yakamata tayi amfani da busheshshen abinchi wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman gabaki daya .

Zuwa awu (Antenatal) yana da amfani sosai wanda alokocin awu za a auna aga yadda yaro ya kwanta a ciki .

Kuma ana auna aga wassu matsaloli masu kashe uwa da jaririnta domin a magance su da wuri.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!