HANYOYIN KASANCEWA CIKIN QAMSHIN JIKI AMARYA DA UWARGIDA
Macen da take so ta riqa yin qamshi mai xaukar hankali sai ta nemi
- Kafi amarya qamshi
- Garin ambar
- Garin miski
- Garin kaninfari
- Kafun-kafun
Sai ta cakuxasu a cikin baslilin (Vaseline) ta ringa shafawa. Duk inda kika je to gurin zai dinga qamshi ba za’a so ki tashi ba.
HANYA TA BIYU
Macen da take so ko ina nata ya ringa qamshi da mijinta ya kusanceta sai yaji tana qamshi sai ta nemi Sandal na itace sai ta nemi turaren ‘yan matan Arewa sai ta nemi lemozin da Dusha sai ta sassara wannan itacen na Sandal sai ki zuba a ciki sai ya kwana uku (3), sai ki xaukoshi turaren ki riqa shafeshi a qirjinki zuwa mara. Shi kuma itacen ki riqa hayaqi da shi. Za kiga inda ko ina aka kusance ki zaki burge mijinki.