MUHIMMANCI, TASIRI DA KUMA ALFANUN JIGIDA A KUGUN MATA
Babban alfanun da jigida yake yiwa mata kamar yadda bincike
ya tabbatar a wannan lokacin shine, yana karawa mace fadin
kugunta ga irin matan nan da suke da karancisa.
Maza da dama da aka zanta dasu sun nuna sha’awarsu na
ganin matansu na aure suna saka jigida domin yana karamusu
kyau musamman idan mace tana sanye da kayan da zasu
bayyanasu.
Har ilayau cikin alfanun da jigida ke dashi shine yakan motsa
sha’awan maza a yayin da suka ji sautinsa ko suka hango
shatinsa.
Kara ko sautin dake fitowa daga jigida a lokacin wasannin
motsa sha’awa da kuma lokacin gudanar da jima’i abune dake
himmanta maza yake kuma kara musu kuzari da azama.
Sai dai duk da wadannan tasiri, mahimanci da alfanun da jigida
ke dasu ba duka mata bane suke sanyawa ba, haka ma maza
da dama basu son ganin mace da jigida. Wasu mutane sun
riga sun kudura cewa duk mace ko budurwar da aka ga tana
sa jigida ko akaji sautinsa a tare da ita suna daukanta mutuniyar banza, wanda yin hakan babban kuskure ne.
Shi dai shan koko daukan rai ne. Abincin wani, gubar wani.