MUHIMMAN HANYOYIN DA ZA A BI DON KARFAFA LAFIYA LOKACIN SANYI
Muhimman Hanyoyin da ya kamata a bi don Karfafa Lafiya lokacin Sanyi.
Dazaran ƙarshen shekara ya nufato, Sai a shiga yanayi na sanyi. Hakan na iya zama kalubale ga lafiyar mutum ta hanya mafi sauƙin kamuwa da mura, tari, bushewan labba, da sauransu.
A kula da waɗan nan shawarwari:
- A yawaita shan ruwa sosai
- A yawaita wanke idanu akai akai domin gujewa kamuwa da ciwon ido.
- A yawaita amfani da abin rufe fuska da hanci (Facemask).
- A takaita zirga-zirga a waje sai dai wanda ya zama dole, mai mahimmanci.
- A yawaita sa kaya masu ɗan kauri, ko rigunan sanyi domin sanya dumi a jiki.
- A yawaita rufe tagogi da kofofin domin takaita shigowar kura daki.
- A yawaita shafa mai a jiki domin dandashe fata kar ta bushe.
- A yawaita shafa mai a labba domin kare su daga farfashewa ko tsagewa.
ABIN LURA: Wannan yanayi na iya tayar ma da masu ciwon Sickler da Athma ciwon su sosai. A kula.