MAGANIN RABUWA DA CIWON ULCER KOMAI TSANANIN TA FISABILILLAH.
DON ALLAH IDAN KA KARANTA KA TURAWA SAURAN YAN UWA.
Ciwon gyambon ciki (ulcer) ciwo ne mai zafi a cikin rufin ciki wanda shi ake kira da (Gastric ulcer)akwai kuma peptic ulcers wanda shine rauni wanda yake faruwa ga karamin hanji ko kuma cikin ciki(babban hanji).
Hakan na faruwa a lokacin da karamin rufin dake kari ciki daga sinadaren dame narka abinci karfin sa ya ragu,hakan zai bada dama ga sinadaren su rika cin gyallen rufin dake cikin ciki,wanda wannan shi ake kira da Ulcer.
ABINDA ZAA NEMA.
- Garin Rumman (Pomegranate)
- Garin Zogale(Moringa)
Kowanne zaa samo kamar chokali 5 zaa hade su waje daya,sai a rika diban rabin chokali zaa hada da ruwa karamin kofi,ko pure water daya da rabi zaa dafa shi.
Bayan an sauke sai a bari ya huce a zuba zuma kamar chokali 1 babba a ciki sannan asha kofi 1 da safe kofi daya da dare,da safe bayan an karya da dare bayan anci abinci, haka har tsawon mako 2(sati 2).
Insha Allah zaa samu waraka.
Allah yasa mu dace.