SIRRUKAN DAKE TATTARE DA CUCUMBER WANDA BA KOWA YASANSHI BA

Cucumber tana da sirruka da dama a tattare da rayuwar dan adam, domin masana kiwon lafiya sun bayar da umarnin a yawaita yin amfani da ita saboda irin sirrukanta a jiki. Kadan daga cikin amfaninta ga rayuwarmu ta yau da kullum sun hada da:

 1. Narkar Da Kitse:
  Duk mai yawan amfani da Cucumber zai rika samun isasshen lafiya, karin ni’imar jiki da kwarjini. Wannan ta sa mata suke yawaita sanya barinta a kan idanuwansu. Dalili a fili ne cewa a daidai lokacin da mace ta sanya Cucumber a kan fuskarta, Cucumber za ta tsotse duk rubabben kitse da ke tattare a kan fatar kwayar idanunta nata, domin tana da wasu sinadaran da ke warkar da irin wadannan cutukan na kan fata. Ba ma a fatar idanu kawai ba, an nuna cewa mutum zai iya gyara Cucumber ya dora kan duk inda yake masa ciwo, ko inda fata ta sami matsala. Sannu a hankali komai zai gushe kuma zai samu waraka nan take.
 2. Kore Yana Da Raba:
  So tari idan mutum ya yi wanka da ruwan zafi, raba za ta rufe duk wani gilashin da ke dakin wankan ko kuma bayan ya fito zai rasa yadda zai kalli madubi sabo irin wannan rabar da yana a wasu lokutan. Daya daga cikin sirrukan Cucumber su ne da arar ka shafa shi a kan gilashin, daga lokacin zai washe kuma mutum ya ci gaba da amfani da kayansa lafiya lau.
 3. Ciwon Kai:
  A duk lokacin da mutum ya sha wahalar aiki ko gajiyar musamman, wadanda ke haddasa nauyin jiki a lokacin da aka tashi daga bacci, muddin ya dan ci Cucumber kafin ya kwanta, zai tashi tamkar wanda ya wuni yana motsa jiki.
 4. Warkar Da Radadi:
  A wasu lokutan mutum ya kan iya samun buguwar wata gaba a jikinsa, har ta kai shi da yin kara saboda da radadin da zai iya ji daga gare shi. Amma a duk lokacin da ki ka shafa Cucumber a wajen da irin wannan radadin ya samu, nan da nan radadin da zafi za su gushe saboda irin sirrin da ke cikin Cucumber.
 5. Share Datti A Kan Bango:
  Kamar yadda muka ambata Cucumber tana da sirruka daban-daban bila-adadin, sai dai mutum ya takaita ga wadanda ya sani kawai. Ko ka san za ka iya amfani da ita wajen share kowane irin nau’i na datti ko zane a bango da yara ke yi da abin rubutunsu? Da zarar ka bare Cucumber ka shafe a kan zanen, zai bace tamkar babu wani zanen da aka taba yi a wajen.
 6. Warkar Da Warin Baki:
  Da yawa daga cikin mutane suna fama da matsalar warin baki. Muddin za su yi magana bakinsu ya rika wari ainun ta yadda ba za a so matsawa kusa da su ba. Idan kina da wannan matsalar kawai ki bare Cucumber, ki sanya a cikin bakinki sai ki rike shi a daidai saman bakin da harshe kimamin Sakan 30. Daga nan ki tofar da ita a kasa. Idan kika luzumci wannan, warin bakinki zai kau ba tare da bata lokaci ba.
 7. Cire Tsatsa:
  Uwarigda da zarar kin lura a cikin kayan girkinki akwai wadanda suka yi tsatsa, maza ki yi amfani da Cucumber, da zarar kin yayyanka ta, kika yi amfani da ita a kan kwanukan. Ba ma goge tsatsar kadai zai yi ba, kin hutar da kanki da yin amfani da wasu sinadaran da za su iya cutar da ‘ya’yanki.
 8. Karin Kuzari:
  A duk lokacin da gajiya ta yi miki yawa, maimakon kwanciya don ki huta, kawai ki yanka Cucumber ki ci kadan, za ki wartsake nan da nan.
 9. Gyara Fatar Fuska:
  Ina masu amfani da mayuka masu lalata fuska ko bata jiki? Da zarar zarar kin yayyanka Cucumber kika dora a wuta ya tausa sosai, kawai ki bude marfin tukunyar sai ki sanya fuskarki don dumin ruwan ya shafi fuskarki. Daga nan za ki ga yadda fuskarki za ta koma ba tare da wata matsala ba.
 10. Wankin Takalmi:
  Idan kika yayyanka Cucumber, za ki iya amfani da shi wajen gyarawa da wanke takalmin maigida. Yin amfani da ita ba kawai za ta sanya takalmin yin sheki ba kawai, za ta tsotse duk ruwan da ke cikin takalmin.

Please share after reading

Don’t edit don Allah

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!