YADDA AKE AMFANI DA SUKARI WAJEN GYARAN FATA (SUGAR)

Asalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin filinmu na kwalliya.

Na san za a yi mamaki idan na ce amfani da sukari a fatar jikinmu na da matukar muhimmanci.

Yadda ake gyaran gashi da ruwan shinkafa
Yadda ake hada madarar ‘yogurt’ ta gida (home made yogurt)
Yanzu zamani ya kawo mu inda mace ba sai ta shiga kasuwa domin neman nau’o’in man gyaran fata ba, daga cikin kicin ma za a iya hada wasu abubuwa da za su magance matsalolin fata.

Don haka ne a yau na kawo muku muhimmancin amfani da sukari a fatar jiki. A sha karatu lafiya.

Domin samun lebba masu sulbi, a zuba ruwa kadan sosai a cikin sukari yadda ruwan ba zai narkar da shi ba, sannan a riqa murza lebban da wannan hadin sukarin domin samun fatar lebba mai sulbi.

Za a iya yin dilka da sukari. A samu sukari mai ruwan kasa sannan a kwaba shi da ayaba sai a rika dirzawa a fatar jiki domin cire matacciyar fatar jiki da kuma samun sabuwar fata mai haske.
Idan ana buqatar samun shekin fata a kafa da wuya da baya, sai a kwaba sukari da man kwakwa ko man zaitun sannan a dage da dirza waxannan bangarorin jikin da na lissafo akalla sau biyu a mako domin samun fata mai sheki a wadannan bangarori.

Sukari na magance gautsin tafin kafa ko faso ko kauje.

A kwaba sukari da man kwakwa sannan a zuba a roba sai a saka tafin kafa a ciki a rika dirza tafin kafar na tsawon minti 10 zuwa 15 domin magance matsalolin kauje ko faso a fata.

Idan an kasance ana da gautsin fatar tafin hannu, sai a rika gauraya sukari da sabulu ana dirzawa a hannu sannan a wanke domin samun fata mai laushi.

Domin rabuwa da gashin kafa, sai a samu sakari mai ruwan kasa, a kwaba da ruwa kadan sai a shiga murza fatar kafa sannan a sanya reza a cire gashin kafa.

Maza masu fama da cututtukan fata idan sun aske gemunsu za su iya amfani da irin wannan hadi domin samun saukin aske gashin baki.

Za a iya amfani da man zaitun da sukari mai ruwan kasa sannan a kwaba a rika shafawa a fatar hannu kafin a shiga wanka. Yin hakan na sanya fatar sheki da laushi da sulbi.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button