Yadda Zaka Gyara Sunanka Na (BVN) Yayi Daidai da Sauran Takardunka

Lallai wannan lamari na BVN ya sanya yan kasa ta Nigeria acikin wani yanayi na rashin jindadi musamman a lokacin da tazama dukkannin wata hada-hada ta kudade na yau da gobe saida ita wannan lamba ta BVNwato Bank Verification Number ita wannan lamba ta kasance idan an sami matsala sunanka da aka bude maka asusun ajiya wato (Bank Account) yasaba da wadannan katinan shaidar da muke dasu National ID Card, Voter’s Card, Driver’s License da International Passport to matsala ta faru

A nan take asusun da kake ajiya zai sankame wato zai tsaya caak! Hanyoyin da akebi domin wannan gyara.

Step 1:- Zaka fara zuwa bankin da aka bude maka Asusun ajiya saika tambayi Customer Care domin suyima bayanin matakan da zakabi domin a gyarama wannan matsala.

Tunda wani zubin gyaran yakasance suna ne yasaba da katin naka da kuma BVN din, Wata matsalar kuma shekarun haihuwane suka saba ko kuma karin wata kalma acikin sunanka ko kuma ragin wata kalmar.

Step 2:- Idan sunan kane yasaba da BVN dinka to wajibine saikayi sabon ID Card wanda yake dauke da sunan da kakeso kodai yakasance International Passport, National ID Card, Voter’s Card, Driver’s License.

Bayan kayi daya daga cikin wadannan katinan shaidar to zakaje kayi takardar kotu wato (Affidavit) sannan kuma sai kaje gidan jarida kasayi feji wanda za’a rubuta tsohon sunanka da kuma sabon da zaka cigaba da amfani dashi, to idan kagama dukkan wadannan abubuwa saika daukeso can-caak saika nufi hanyar bankin dasu kana zuwa saika mikawa Customer Care ka kara yimusu bayani to shikenan sai a gyara maka.

Step 3:- Idan sunanka najikin katinka da wanda yake ajikin BVN dinka daidai suke amma shekarun haihuwa sun saba da juna to ita wannan matsala ba saikaje gidan jarida ba ko canja sabon ID Card ba ita wannan ana gyarawa ne da takardar kotu ta gyaran shekarar haihuwa ta koma daidai dana jikin katin naka idan kayi wannan saikaje bankin za’a gyara maka wannan matsala cikin sauki.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button