YADDA ZAKU HADA SABULUN KURAJE DA FIDDA TABON FUSKA

 • asef soap
 • pharmaderlm soap
 • kanwa
 • jar dilka
 • Zuma
 • lemon tsami

Ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba
kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, kinkwaba dilka da ruwan zafi cikin cokali cin abinci daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa Zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki kamar ya rage minti biyar kafin ki shiga wanka, Indan kin shiga wanka sai ki kuma wanke fuskarki da sabulun kamar uku ko Dama da haka.

SABULUN FIDDA TABO

ko Zuma Zaki Iya shafawa idan Zaki kwanta bacci sai da safe ki wanke da ruwan dumi.

 • misscoroline soap
 • shary soap
 • aloevera soap
 • garin alkama
 • zuma
 • kanwa kadan
 • lemon tsami Bari 1/1

Sai ki goga su ki hada ki zuba Zuma a ciki da lemon tsami da kanwarki ki kwaba, ki dinga shafawa fuskarki minti biyar kafin ki shiga wanka, idan kuma zakiyi wanka dashi Zaki dinga wanke fuskrki.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!