HANYOYIN GYARA GASHI yayi tsawo

  • Gashi na daga cikin abubuwa da suka fi daukan hankalin namiji a jikin mace. Namiji kan ji farin ciki a yayinda ya kalli ko ya taba gashin uwargidanshi musanman idan gashinta ya kasance mai sheki ne tare da laushi sannan kuma baki.
  • Akwai hanyoyi da dama na gyaran gashi, zamuyi bayaninsu daya bayan daya:
  • Amfanida tafarnuwa da man zaitun: yanda zakiyi saiki samu tafarnuwan da dan yawa kamar sama da goma saiki baresu ki yanyanka sannan ki jikasu da man zaitun saiki bari yayi kwana uku ajike saiki soya ki ajiye kina shafawa akayi bayan awa daya a wanke.
  • Amfanida man amla da man kwakwa da zuma: yanda akeyi shine zaki zuba man amla kadan zuma itama idan amla ya zama cokali hudu to zuma ya zama zuma cokali biyu man kwakwa shima cokali biyu saiki zuba a ruwan zafi shi kuma kamar cokali hudu a gauraya kamar idan za’ayi shampoo sai ashafa akayi bayan mintuna talatin shikenan sai kiyi shampoo dinki.
  • Amfani da man kwakwa da man amla: Daga farko ki dora man kwakwa a wuta sannan sai ki zuba masa man amla. Daga nan sai ki gauraya sosai, idan kin tabbata sun gaurayu, sai ki sauke daga wuta, har hadin ya huce. Sai ki zuba man a kwalba ko murta. Kina shafa wannan hadin a fatar kanki da gashinki kamar sau uku a sati.
  • Amfani da lemon tsami: Ki samu ruwan lemun tsami, sai ki hada shi da kwai da kuma man amla. Sai ki shafa hadin a fatar kai da kuma gashi. Ki bar hadin a kanki har tsawon minti talatin, sannan ki wanke da ruwan dumi. Za ki iya yin wannan hadin sau biyu a wata.

Amfani da aloe vera: Ki samu ruwan Aloe bera, sai ki shafa a fatar kai da kuma gashi, bayan minti ashirin sai ki wanke da ruwan dumi.

Amfani da man zaitun: Man zaitun na sanya gashi ya yi baki, taushi da kuma tsawo. Za ki iya mayar da man zaitun ya zama man kitsonki.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!