YADDA UWARGIDA ZATA HADA TEA SPICES
Abubuwan bukata
- Chitta 2cups
- Kanumfari 2spoons
- Naa’naa 1/2 cup
- Ganyan Lipton me flavor din da kikeso 3
- Kirfa 1/2 cups
Yadda za’a hada
Ki tabbata dukka a bushe suke,se ki daka su suyi luqwui
Ki samu tukunya ko kasko me zurfi ki juyesu dukka a ciki
Ki dora akan wuta kina juyasu kar ki bar juyawa har na minti 5
Tea spices dinki ya hadu
Yadda yakeda yawan nan zaki iya zubashi a roba me murfi ki rufe dan amfanin gida,zakuma ki iya fara sanaa dashi.