LEMON TSAMIYYA (Tamarind Juice)
Abubuwan bukata
- Tsamiyi
- Suger
- Kanunfari
- Citta
- Lemon tsami
Yadda za’a hada
Da farko uwargida Zaki dafa sugarki da ruwa kamar kofi daya saiki barshi ya huce ,ki dakko tsamiyarki ita ma ki dafa ta da ruwa da kanunfari da citta ,bayan ta dahu sosai saiki tace ruwan ki barshi ya huce ,saiki yanka lemon tsamin ki guda biyu ki matsa a ciki ,saiki dakko ruwan sugerki shima ki zuba a kai ruwan tsamiyan saiki juya sosai asa a fridge idan yayi sanyi sha Dadi lfy . mungode