Yadda za a rabu da kaushin kafa lokacin sanyi

Tafin kafarmu na daya daga cikin sassan jikinmu da ya kamata mu rika kulawa da shi, kasancewar idan ba a yi hanzarin magance kaushin kafa ba, sai ya zarce faso.
Ta yaya za ki gane kina da kaushin kafa? A lokacin da kika fara jin tafin kafarki na janyo audugar jikin kujerar daki ko bargon da kike lullubuwa da shi, ko kuma yana kama kaya ko na gogar jikinki, idan kika ji haka to kina da kaushin kafa.
Mutane da dama na son rabuwa da wannan matsalar don haka ne muka kawo miki hanyoyi da za ki bi don rabuwa da kaushin kafa.

Ki zuba ruwan dumi a cikin bokiti ko wani abu mai fadi, sannan ki sanya kafarki a ciki
Bayan tafin kafarki ya juku, sai ki cire daga ruwan dumin, daga nan ki dauki dutsen goge kafa, sannan ki rika goge tafin kafarki wurin da yake da kaushi. Ki rika zagaya dutsen a wuraren da kaushin ya fito, daga nan ki sake mayar da kafarki cikin ruwan dumi
Bayan kamar minti 15 sai ki sake goge tafin kafarki da dutsen goge kafa domin cire fatar da ta mutu a tafin kafarki
Daga nan ki wanke tafin kafarki da sabulu a cikin ruwa. Bayan nan sai ki cire kafarki, sannan ki goge da tawul
Daga nan ki shafa man tafin kafa, idan ba ki da shi sai ki shafa man baseline
Bayan nan sai ki sanya safa, sannan ki sanya kafarki a cikin leda, bayan ki daure sai ki kwanta barci. Ba za ki kwance ba sai washegari.

GYARAN KAFA

  • SHAMPOO DA GISHIRI kisamu ruwan dumi daidai yadda baxaki kona kafarkiba, kixuba shampoo da gishiri acikin ruwan, kisanya kafafunki aciki natsawon minti shabiyar. Sannan saiki wanke kafar tas idan ta bushe kishafa man zaitun
  • MAN RIDI DA MANKWAKWA
  • Kihadasu wuri guda kichakuda, dadare kishafa akafafunki kisanya safa akafar xuwa safe, saiki wanke da ruwan dumi, idantabushe kishafa man zaitun ko man ridi
  • MAN ALAYYADI DA DANYEN MANSHANU
  • Kihadesu wuri guda kitabbatar sunhade jikinsu saiki shafa akafarki dadare xuwa safe

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!