YADDA ZA’A MAGANCE WARIN BAKI

Sau da yawa za ki ga baki yana wari musamman ga wadanda ba su ci abinci ba.

Wani duk da ya wanke bakinsa da magogi da man goge baki, hakan ba ya hana shi warin baki.

Kuma galibi irin wadannan mutane ba sa sanin cewa, bakin nasu yana wari.

Saboda haka idan kana son ka san cewa bakinka yana wari ga irin abin da za ka yi don tabbatar da bakin yana wari:

Ka lashe bayan hannunka sai ka jira na tsawon minti 10 sannan sai ka sinshina.

Bude baki ka fitar da iska sai ka tare iskar da hannu sannan ka sinshina in da wari to kana da warin baki.

Ka tambayi amini ko aminiyarki ko maigida da kuma ’ya’ya don sanin ko kina da warin baki.

Abubuwan da suke rage warin baki:

Cin cingam mara sukari; cin cingam na rage warin baki musamman wanda ba ya da sukari.

Ki tabbatar da cewa, cingam din ba ya da sukari don in akwai sukari zai sa baki wari don bakteriya da take bakinmu tana son sukari kuma yin haka zai sa bakin wari sosai fiye da na da.

Shan ruwa sosai: Busasshen baki yana wari. Shi ya sa baki ya fi wari da safe don bakin ya jima a rufe ba tare da ya ci wani abu ba.

Shan ruwa yana rage warin baki. Kada ki bar bakinki a bushe.

Ki ci ayaba; Idan kina kokarin rage kiba ne, za ki iya cin ayaba, in da hali da yawan cin ’ya’yan itace. Yin hakan na rage warin baki.

Wanke bakinki a kan lokaci: Ki zama mai wanke bakinki da safe da yamma don rage warin baki.

Akwai lunguna da yawa wadanda abinci yake makalewa a kan hakora. Babban abin da yake janyo warin baki shi ne barin ragowar abinci a lungunan hakora.

Wanke baki na da muhimmanci sosai in ba ki yi haka ba za a guje ki.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!